Idan na yi magana kan 'yan bindiga, kawuna za su gwaru, inji Sanatan Arewa
- Wani sanata mai wakiltar kudancin Kaduna ya bayyana rashin ji dadinsa game da ayyukan 'yan bindiga
- Ya bayyana cewa, idan ya bude baki ya yi magana game da 'yan bindiga za a samu gwaruwar kai
- Ya kuma bayyana cewa, wadanda suka kawo 'yan bindiga su ne kadai za su iya korarsu daga yankunan
Kaduna - Dan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu, Danjuma La’ah, ya bayyana dalilan da ya sa ya zubar da hawaye a lokuta daban-daban a farfajiyar majalisa yayin da yake gabatar da kudiri kan hare-haren ‘yan bindiga a mazabarsa.
Dan majalisar na tarayya ya bayyana cewa wasu daga cikin abokan aikin sa na sanata suna tunanin ayyukan ta'addanci a Kudancin Kaduna batu ne na kudancin Kaduna kadai, SaharaReporters ta ruwaito.
Da yake magana, ya tuna lokacin da ya fada wa sanatoci cewa, akwai lokacin da dukkan mazabu 109 na sanata a kasar za su fuskanci matsala irin ta yankinsa, inda kuma ya ce yanzu hakan ya faru.
Ya ce:
“Na sharbi kuka marar adadi, amma na san lokaci zai zo kuma lokacin ya zo domin yayin da nake kuka a zauren lokacin da nake gabatar da kudiri kan bindiganci a Kudancin Kaduna, na ce wata rana ko ta yaya, wadannan abubuwan za su shafi kowannen mu.
“Domin muna tunanin cewa kawai lamarin ya shafi Kudancin Kaduna ne, amma ku gaya mani wace jiha ce a cikin wannan kasar da 'yan bindiga ba su shafa ba?
“’Yan bindiga ba su da abokai, ba su san kabilu ba; ba su san addini ba. Kowa, kai ne kuma idan suka same ka, batun kudi ne.”
Dan majalisar ya ce bayan da ya gabatar da kudiri kan rashin tsaro a Kudancin Kaduna sau da yawa, ya daina magana, yana mai cewa idan ya ci gaba da magana bisa abin da ya sani:
"Kawuna za su gwaru kuma duniya ma za ta juya yamutse. Don haka, ya fi kyau in bar batun na kame baki na.”
Ya ce ayyukan 'yan bindiga a Kudancin Kaduna ba sabon abu bane, yayin da yake fatan cewa a ci gaba da yaki da masu aikata manyan laifuka a Arewa, wadanda suka kirkira da horar da 'yan bindiga su ne za su iya korar su.
Ya kara da cewa:
"Duk wadannan abubuwan ba sabbi ba ne. 'Yan bindiga, 'yan Boko Haram da masu tayar da kayar baya kuma har yanzu ba a canza wani yunkuri daga abin da ke faruwa ba. Za mu iya yin addu'a ne kawai. Wadanda suka kirkire su a can ya kamata su kasance mutanen da za su zo su kore su daga wannan wuri.”
Kasurgumin shugaban 'yan bindiga ya tona asirin 'yan uwansa, ya nemi gafara
Goma Samaila, shugaban gungun masu garkuwa da mutane a yankin Rigachukum ta jihar Kaduna, ya bayyana sunayen mambobin kungiyar sa, Daily Trust ta ruwaito.
Mutumin mai shekaru 47, wanda rahotanni ke cewa ya dade yana tafka ta'annuti, ya yi magana kan wasu ayyukansa da adadin kudin da ya karba a matsayin kudin fansa.
A wani faifan bidiyo, an ga Samaila yana rokon gafara yayin da daya daga cikin jami'an tsaron da ya kama shi ke tambayarsa.
Ya ce:
“Ina rokon jinkai da gafara; Ba zan sake aikata irin wannan laifin ba."
Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara
A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.
Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.
Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.
Asali: Legit.ng