Datse sadarwa: 'Yan bindiga na amfani da layikan Nijar wurin kai farmaki, Dan majalisa

Datse sadarwa: 'Yan bindiga na amfani da layikan Nijar wurin kai farmaki, Dan majalisa

  • Dan majalisar jihar Sokoto ya ce 'yan bindiga sun koma amfani da layikan sadarwan Nijar wurin kai farmaki
  • Aminu Almustapha Gobir ya ce hatta shi da kanshi ya samu barazanar 'yan bindiga cewa za su kai masa da yankinsa farmaki a Sokoto
  • Ya sanar da cewa miyagun sun kai farmaki sansanin soji da ke Dama a karamar hukumar Sabon Birni har sun sheke sojoji 12

Sokoto - 'Yan bindiga suna yin amfani da kafofin sadarwa na jamhuriyar Nijar wurin kai farmaki kamar yadda Aminu Almustapha Gobir, dan majalisa mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta arewa a majalisar jihar Sokoto.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daga cikin hanyoyin magance matsalolin 'yan fashin bindiga, gwamnatin Najeriya ta datse dukkan hanyoyin sadarwa a jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina.

Kara karanta wannan

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

Datse sadarwa: 'Yan bindiga na amfani da layikan Nijar wurin kai farmaki, Dan majalisa
Datse sadarwa: 'Yan bindiga na amfani da layikan Nijar wurin kai farmaki, Dan majalisa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Hakan an gano cewa ya datse sadarwa tsakanin 'yan bindigan da masu kai musu bayanai.

Amma a matsayin hanyar cigaba da aiwata ta'asa, 'yan fashin sun koma amfani da kafofin sadarwa na kasashe da ke makwabtaka da ke da Najeriya ta Sokoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gobir ya ce shi da kan shi ya samu barazana daga wani dan bindiga da ke amfani da layin sadarwa na kasar Nijar.

"Dan fashin dajin ya na min barazanar cewa zai jagoranci tawagar sa domin su kawo min farmaki da yanki na," ya sanar da Daily Trust.

Gobir ya kara da tabbatar da farmakin da 'yan fashin suka kai sansanin sojoji da ke karamar hukumar Sabon Birnin ta jihar.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu 'yan bindiga suka kai samame sansanin soji inda suka kashe jami'in tsaro tare da banka wa tankar fetur wuta.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Shinkafi Bayan Tura Wasiƙa, Sun Kutsa Ofisoshin 'Yan Sanda Sun Saci Bindigu

"Da gaske ne sun kai farmaki sansanin soji da ke Dama kumaa sun kashe 12 daga ciki yayin da wasu suka bace har yanzu.
“A saboda haka ne na ke ganin laifin gwamnati da ta rufe layikan sadarwa a yankin gabashin jihar ba tare da bada sojoji isassu domin mamaye wurin ba.
“'Yan fashin dajin na amfani da layikan sadarwa na Nijar domin sadarwa a tsakaninsu tare da aiwatar da miyagun ayyukansu.
“Na yi tsammanin gwamna zai samarwa 'yan sanda da sojoji wayar Thuraya wacce za ta basu damar sadarwa tsakaninsu da manyansu idan suna bukatar taimako inda babu layikan.
“Hakan gwamnan Zamfara yayi kuma tabbas kwalliya ta na biyan kudin sabulu," yace.

Daga bisani, NYSC ta ce ita ta fitar da shawarar biyan kudin fansa, za ta fara bincike a kai

A wani labari na daban, a abinda da ya janyo wa hukuma NYSC cece-kuce, ta aminta da cewa daga cikin takardun bayanai kan tsaronta ne ga ma'aikata da kuma 'yan bautar kasa aka samu wannan shawarar wacce ta matukar tada kura.

Kara karanta wannan

Gobara ta yi kaca-kaca da Hedkwatar hukumar NPA, dukiyoyi sun kone kurmus

Shawarar ta bukaci duk masu hidimar kasa da kuma ma'aikata masu kaiwa da kawowa kan manyan tituna da ke da hatsari da su sanar da iyaye, 'yan uwa da abokan arziki ko kuma wadanda za su iya biyan kudin fansarsu idan an sace su.

Hukumar ta ce ta gaano cewa tabbas wannan takardar ta gama yawo a gari amma akwai wadanda babu wannan shawarar a ciki, Premium Times ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel