Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari

Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari

  • Hadin gwiwar kungiyoyin Arewa sun bayyana rashin jin dadi ga yadda aka zargi Abba Kyari
  • Sun bayyana cewa, sam ba a yi masa adalci ba tunda ba a ji ta bakinsa ba aka dakatar da shi
  • Sun kuma bukaci a sauya tsarin yadda ake tafiyar da tuhumar don bin ka'idar da ta dace dashi

Hadin gwiwar Kungiyoyin Arewa sun yi zargin cewa cibiyar bincike ta FBI da rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) sun take hakkin Abba Kyari kai tsaye na bincikensa da ake.

A cewar kungiyar, Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda (DCP), ba a ba shi damar yin bayani ba kawai FBI da NPF suka dauki matakin gaggawa a kansa.

Kungiyar tana son a canja shari’ar Abba Kyari

Don haka, sun nemi a gaggauta duba dakatarwar Kyari sannan a mika shari'arsa ga Hukumar Leken Asiri ta Najeriya.

Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari
DCP Abba Kyari | Hoto: Abba Kyari
Asali: UGC

Bukatar tana kunshe ne cikin sanarwar da aka bai wa manema labarai a karshen taron da kungiyar ta yi a Kaduna.

Ga kadan daga cikin sanarwar da Legit.ng ta gani ya ce:

"Tattaunawa ta musamman ta lura da lalatattun hanyoyin da ke da alaka da sabawa ka'idojin kasa da kasa a kokarin FBI na sanya DCP Kyari a cikin lamarin Hushpuppi, da kuma hanzarin da hukumomin 'yan sandan Najeriya ta yi na cire shi daga mukaminsa tare da maye gurbinsa nan da nan.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa, ya kamata FBI ta tuntubi hukumomin Najeriya da ke kasar Amurka ko nan Najeriya don jin ta Abba Kyari kafin bayyana zargin.

A cewarta:

"An keta alfarma da sakaci kan tsarin yayin da FBI ta yi gaggawar buga zargin da ake ta yanar gizo ba tare da fara sanar da hukumomin Najeriya ba."

Majalisar wakilai ta magantu kan karrama Abba Kyari da ta yi a matsayin gwarzo

Majalisar wakilai ta ce Abba Kyari zai ci gaba da kasancewa mai mutunci a idon majalisa har sai an same shi da laifin tuhumar da hukumar bincike ta FBI da ke Amurka ta yi masa.

Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta dakatar da Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda bisa shawarar Sufeto Janar na 'yan sanda IGP, Usman Baba, har zuwa lokacin da hukumomin 'yan sandan Najeriya za su gudanar da bincike akansa.

Majalisar wakilai ta karrama Abba Kyari a watan Yunin bana

A watan Yunin 2020, majalisar wakilai sun karrama Kyari haifaffen jihar Borno saboda kyakkyawan aikin da ya yi wa rundunar 'yan sandan Najeriya da ma Najeriya baki daya.

Gayyatar da karramawar ta biyo bayan bukatar da dan majalisar da ke wakiltar mazabar tarayya ta Chibok a jihar Borno, Ahmad Jaha, ya gabatar kwanaki biyu kafin zuwansa majalisar.

Lokacin da jaridar Punch ta tuntube shi don yin magana kan karramawar da aka yi wa Kyari, bayan da aka zargi dan sandan da aikata abin kunya, Benjamin Kalu, ya ce DCP har yanzu bai da laifi har sai an tabbatar da laifinsa.

Ofishin ministan shari'a ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

A wani labarin, Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, kuma ministan Shari'a Abubakar Malami, ta ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.

Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch.

FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a Amurka, bayan kame masa wani abokin harkallarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel