Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna

Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna

Andy Ubah, dan siyasan Najeriya da kasar Amurka da Ingila ke tuhumarsa kan sumogal din daloli na dab da zama gwamnan jihar Anambra.

Kasar Amurka ta binciki Uba kan wani al'amari da ta alakanta da damfara kamar yadda gwamnatin Amurka ta sanar, Premium Times ta wallafa hakan.

Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna
Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Andy Ubahm dan takarar gwamna a Anambra. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

A Ingila inda aka haramta masa shiga, hukumomi sun ce dan siyasan Najeriya na da alaka da damfara da wasu al'amuran zargi kuma Ingila ba ta da bukatar ganin shi a kasar.

Uba shi ne dan takarar jam'iyyar APC a zaben 6 ga watan Nuwamba na gwamnan jihar Anambra, jihar da ke kudu maso gabas na kasar nan.

An taba rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar sa a 2007 amma kotun koli ta soke zaben saboda Peter Obi, gwamnan jihar a lokacin bai kammala wa'adin mulkinsa ba.

Kara karanta wannan

Hushpuppi: IGP ya mika tuhuma ga Abba Kyari, Malami na duba bukatar mika shi Amurka

Uba a lokacin dan jam'iyyar PDP ne, Premium Times ta ruwaito.

A matsayinsa na hadimin shugaban kasa Olusegun Obasanjo a lokacin, ya na daya daga cikin manyan 'yan siyasa a lokacin.

U. S. ta tuhumesa

Uba wanda aka sani da Emmanuel Uba ya fada tashin hankali da hannun gwamnatin Amurka a 2003 sakamakon shigar da $170,000 cikin Amurka yayin da ya yi amfani da jirgin fadar shugaban kasa wanda ya sauka a New York domin wani taron majalisar dinkin duniya.

Ya boye kudin kuma bai bayyana su a filin jirgin sama na John F. Kennedy ba kuma daga bisani ya mika shi ga budurwarsa, akasin dokar kasar Amurka wacce kuma ya na da masaniya a kai kamar yadda takardun kotu da gwamnatin Amurka ta bayyana.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige shugaban cocin Anglika har lahira a Imo

Gwamnatin U. S. ta kwace kudin bayan ta bi tsarin shari'a wanda Uba da budurwarsa Loretta Mabinton suka samu wakilcin lauyoyinsu.

U.K ta tuhumi Uba

Uba ya fada wani rikici da gwamnatin UK kuma ta hana shi shiga kasar Turai.

"A sakamakon dabi'ar ka da kuma tu'ammalin ka da damfara, ba a bukatar ganin ka a UK kuma sakataren kasar ya yanke hukuncin cewa kada ka sake shigowa kasar," hukumomin UK suka sanar da Uba a ranar 2 ga watan Disamban 2008.

Duk da haramta masa shiga UK, Uba ya yi yunkurin shiga kasar a ranar 24 ga watan Disamban 2008 a jirgin da ba na haya ba.

Hukumomin UK sun bukaci ya juyo gida Najeriya bayan saukarsu a filin jiragen sama na London Luton bayan kwace kudi tsaba da suka kai €135,000 daga wurinsa.

Hukumomin UK sun tabbatar da cewa ya sauka kasar dauke da kayan karau na zinarai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

Gwamnatin UK ta ce ta na zargin kudin da fitowa daga wani al'amari na laifi ko kuma za a aikata wani laifin da su.

Sojojin Najeriya sun sheke 'yan fashin daji 42 a yankin Shiroro da ke jihar Niger

A wani labari na daban, jami'an tsaron Najeriya da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun sheke miyagun 'yan fashin daji 42 a yankin Alawa da ke Shiroro a jihar Neja.

PRNigeria ta tattaro cewa, jami'an tsaron hadin guiwar sun kai wa 'yan bindigan samame yayin da suka gudo daga jihar Zamfara inda sojoji suka matsa musu da luguden wuta.

Wata majiya da ke da hannu cikin aikin ta sanar da PRNigeria cewa, sakamakon musayar wutan da aka yi, soja daya ya rasa rayuwarsa yayin da wani ya samu rauni.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel