Babban magana: Boko Haram sun fara koya wa 'yan bindiga yadda ake harbo jirgin sojoji

Babban magana: Boko Haram sun fara koya wa 'yan bindiga yadda ake harbo jirgin sojoji

  • Rahotannin tsaro da muke samu daga majiyoyi daban-daban sun bayyana yadda Boko Haram ke horar da 'yan bindiga
  • A halin da ake ciki, ana zargin wasu mayakan Boko Haram na ci gaba shigowa yankunan Arewa maso yamma
  • An suna kitsa yadda ake sace mutane da kai hare-hare kan mazauna daban-daban a yankunan

Kaduna - 'Yan Boko Haram sun fice daga sansanin su a Arewa maso Gabas don hada karfi da 'yan bindiga a Arewa maso Yamma, inda suke gudanar da horon makamai da garkuwa da mutane, kamar yadda majiyoyin soji suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Juma'a.

Kungiyar Boko Haram na kara neman hadin kai da kungiyoyin ta'addanci tun bayan mutuwar shugabansu Abubakar Shekau a watannin da suka gabata, inji rahoton Punch.

Kungiyar ISWAP na shiga yankunan Boko Haram, inda take yakar masu biyayya ga Shekau, lamarin da ya kai har wasu ke mika wuya ga ISWAP din ko sojin Najeriya.

Read also

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da malami a Kaduna

Babban magana: Boko Haram sun fara koya wa 'yan bindiga yadda ake harbo jirgin sojoji
'Yan Boko Haram | Hoto: prnigerian.com
Source: UGC

Wasu majiyoyin soji guda biyu sun ce wani bangare mai biyayya ga Shekau da ke jihar Borno ya tura kwamandoji biyu da mayaka 250 zuwa dajin Rijana da ke arewa maso yammacin jihar Kaduna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk kwamandojin biyu suna kawance da Bakoura Buduma, wani shugaban Boko Haram wanda har yanzu yake biyayya ga Shekau kuma mayakan sa suna adawa da hadin kan ISWAP, a cewar majiyoyin tsaro.

Daya daga cikin majiyoyin soji ya ce "su ne suke kitsa wasu sace-sacen da ake yi a yankin Arewa maso Yamma."

Majiyoyin biyu sun ce mayakan na Boko Haram suna kuma horar da gungun 'yan bindiga, da aka fi sani da 'yan fashin daji a yankin yadda za su harbo makamai masu saukar ungulu da abubuwan fashewa da sauran makamai.

Ba a iya samun jin ta bakin kakakin rundunar soji ba. Jami'an jihar Kaduna suma ba su mayar da martani nan take ba kan bukatar tabbatar da lamarin.

Read also

Yan Boko Haram sun fara horar da yan bindiga a Kaduna, Majiyoyi daga gidan Soja

Sanarwar wata hukumar tsaro ta Najeriya a farkon wannan watan ta yi gargadin cewa wani kwamandan Boko Haram da sojojinsa na kasa na hijira daga sansanin su a jihar Borno zuwa jihar Kaduna a Arewa maso Yamma.

Manazarta sun ce akwai alamun da ke nuna cewa masu 'yan Boko Haram da 'yan bindigan suna habaka alaka mai zurfi inda duka biyun suka tsaya don samun hanyoyin samun makamai da aikata ta'addanci

Arewa maso Yammacin Najeriya ta dade tana fama da gungun 'yan bindiga, amma a bana, hare-hare da garkuwa da mutane sun karu.

Sojin Najeriya sun cafke kasurgumin shugaban 'yan bindiga mai suna Goma Sama'ila

Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar cafke shugaban ‘yan bindiga da barayin shanu, Alhaji Goma Sama’ila.

Legit.ng Hausa ta tattaro daga jaridar SaharaReporters cewa, an damke Samaila ne a jihar Kaduna da yammacin Juma’a 24 ga watan Satumba.

Rahotannin shaidun gani da ido sun nuna cewa Sama’ila ne ke da alhakin shirya satar shanu da dama a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Read also

Sojin Najeriya sun dakile farmakin da Boko Haram suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe

An ce yana cikin wasu ayyunkan barna na garkuwa da mutane da dama a fadin jihohin.

Jihar Kaduna tana ci gaba da shan fama da barnar masu garkuwa da mutane, kisan gilla da satar shanu daga 'yan bindiga.

Wata majiya ta ce: “Sojojin Najeriya sun cafke Goma Sama’ila, daya daga cikin “ wadanda ake nema” kuma kasurguman shugabannin 'yan bindiga da ke addabar Zamfara, Kaduna, Katsina da sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan ci gaba na zuwa ne yayin da sojoji ke aikin kakkabe 'yan ta'adda a yankin

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.

Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.

Read also

'Yan fashin daji ne ke kewaye da mu, Al'ummar Kaduna sun koka

Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.

Source: Legit.ng

Online view pixel