Yan Boko Haram sun fara horar da yan bindiga a Kaduna, Majiyoyi
- Yan Boko Haram sun fara baiwa yan bindiga horo a cikin dazukan Kaduna
- Wannan ya biyo bayan bankado yadda yan Boko Haram ke komawa jihar Kaduna da DSS tayi
- An ankarar da jami'an tsaro su mike tsaye tun da wuri kan abu yayi tsauri
- Fiye da shekaru 10 kenan Najeriya na fama da rikicin yan ta'addan Boko Haram
Wasu gungun yan Boko Haram sun garzaya Kaduna daga Arewa maso gabas domin fara horar da yan bindiga masu garkuwa da mutane a Arewa maso yammacin Najeriya.
Majiyoyi biyu daga gidan Soja sun bayyanawa Agence France Presse (AFP) ranar Juma'a yan Boko Haramun na horar da yan bindiga wajen amfani da makamai.
Wannan alamu ne dake nuna cewa an fara shirin hadin kai tsakanin yan Boko Haram da yan bindiga.
Majiyoyin sun bayyana cewa yaran Shekau dake Borno sun tura kwamandoji biyu da mayaka 250 dazukan Rijana dake Kaduna.
Dukkan kwamandojin na da alaka da Bakoura Buduma, wani babban jagora karkashin Shekau kafin mutuwarsa.
Daya daga cikin majiyoyi yace:
"Suke daukan nauyin wasu sace-sace jama'a da ake yi kwanakin nan a Arewa maso yamma."
Yan Boko Haram sun fara komawa Kaduna daga Sambisa, Hukumar DSS
Hukumar DSS tace yan Boko Haram sun fara guduwa daga dajin Sambisa dake jihar Borno zuwa karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
A cewar Punch, an samu wannan labari ne a takarda mai take, 'Karin bayani na komawaryan ta'adan Boko Haram zuwa Rijana a jihar Kaduna.' tare da sa hannun DCG B.O Bassey, mataimakin kwamandan bincike na hukumar NSCDC.
A cewar takardar, wasu manyan yan Boko Haram na shirin hada kai da wani Adamu Yunusa da mabiyansa.
Saboda haka hukumar DSS ke ankarar da jami'an tsaro su farga.
Asali: Legit.ng