Dalilin da yasa jam'iyyar PDP zata lashe manyan zaɓuka a 2023, Mataimakin Gwamna

Dalilin da yasa jam'iyyar PDP zata lashe manyan zaɓuka a 2023, Mataimakin Gwamna

  • Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta ɗauko hanyar kwace mulki daga hannun APC
  • Tela yace tun daga shekarar 1999 zuwa yanzun jam'iyyar ta PDP a shirye take kuma kullum kara karfin take
  • Mataimakin gwamnan ya yi kira ga magoya bayan PDP da su kasance a shirye wajen tabbatar da nasarar jam'iyya a babban zaɓen 2023

Bauchi - Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, ya bayyana yaƙinin cewa jam'iyyar PDP zata lashe zaɓukan da za'a yi a babban zaɓen 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Tela ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a kan zaɓen gundumomi na jam'iyyar PDP a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Mataimakin gwamnan yace jam'iyyar ta PDP tana da ƙarfin da zata lashe kashi 70% cikin 100 na zaɓukan dake tafe a matakin kasa da jihohi.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: An kori shugabar mata, tsohon minista da wasu jiga-jigai a PDP

PDP Zata lashe zaɓen 2023
Dalilin da yasa jam'iyyar PDP zata lashe manyan zaɓuka a 2023, Mataimakin Gwamna Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Wane shiri jam'iyyar PDP ta yi?

A jawabinsa, Mataimakin gwamnan yace:

"Daga shekarar 1999 zuwa yau, koda yaushe PDP a shirye take domin a kullum ƙarfin jam'iyyar ƙara karuwa yake yi."
"Ina mai tabbatar muku da cewa a babban zaɓen dake tafe na 2023, jam'iyyar PDP ce zata lashe kashi 70% na kujerun siyasa a matakin jihohi da kuma kasa."

Ya zaɓen gundumomin PDP ya gudana?

Mataimakin gwamnan, wanda shine baturen zaɓen gundumomin PDP a jihar Adamawa, yace an gudanar da zaɓen lami lafiya.

Ya kara da cewa PDP ta gudanar da zaɓen ne a bisa tanajin kundin dokokin da aka kafa jam'iyyar kansu.

"Mun yi farin ciki kan yadda mutane suka fito kwansu da kwarkwata wajen wannan zaɓen, kuma duk abinda sakamako ya nuna shi zamu kai rahoto ga hedkwata."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Zata Lashe Zaɓen Kananan Hukumomin Jihar Nasarawa, Kakakin Majalisa

Daga ƙarshe, ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar PDP, su kasance a shirye kuma a ankare domin tabbatar da nasara a babban zaɓen 2023.

A wani labarin na daban kuma Gwamnan Sokoto ya bayyana matakin da zai ɗauka kan makarantun Almajirai na haddar Alkur'ani

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yace gwamnatinsa zata yi aikin gyaran makarantun Almajirai, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Da yake jawabi ranar Asabar, a wurin rufe taron ƙara wa juna sani kan makarantun almajirai, Tambuwal yace gwamnatinsa zata yi iyakar bakin kokarinta wajen tabbatar da wannan gyara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262