Gwamnan Sokoto ya bayyana matakin da zai ɗauka kan makarantun Almajirai na haddar Alkur'ani

Gwamnan Sokoto ya bayyana matakin da zai ɗauka kan makarantun Almajirai na haddar Alkur'ani

  • Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, yace gwamnatinsa zata gudanar da gyara a ɓangaren makarantun Almajirai
  • Gwamnan yace babu dalilin da zaisa gwamnatinsa na hana karatun neman ilimin Alkur'ani a jihar
  • Gwamnatin tarayya ta yaba da tsarin da gwamnatin jihar Sokoto ta ɗauka na yin kwaskwarima a ɓangaren

Sokoto - Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yace gwamnatinsa zata yi aikin gyaran makarantun Almajirai, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Da yake jawabi ranar Asabar, a wurin rufe taron ƙara wa juna sani kan makarantun almajirai, Tambuwal yace gwamnatinsa zata yi iyakar bakin kokarinta wajen tabbatar da wannan gyara.

Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal
Gwamnan Sokoto ya bayyana matakin da zai ɗauka kan makarantun Almajirai na haddar Alkur'ani Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamnan yace:

"Ba mu da shirin hana karatun tsangaya na haddar Alkur'ani, domin wasu mutane sun fara rokon Sokoto ta bi sahun sauran jihohi."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi albishir a taron UNGA, yace rashin tsaro yana shirin zama tarihi a Najeriya

"Muna kokarin nemo hanyoyin warware duk wasu ƙalubale da karatun tsangaya yake fuskanta, kuma mun ɗauki damarar yin hakan, domin lokaci ya yi."

Tambuwal ya ƙara da cewa gyara makarantun Almajirai zai taimaka sosai wajen rage yaran dake gararanma ba tare da zuwa makaranta.

Sarkin musulmi ya yi kira ga FG

A jawabinsa, Mai marataba sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, ya shawarci gwamnatin tarayya da hukumar bada ilimin bai ɗaya (UBEC) cewa su tallafawa tsarin makarantun tsangaya na almajirai da kuɗaɗe.

Hakazalika ya shawarci sauran jihohi da su kwaikwayi gwamnatin Sokoto, wajen ɗaukar matakan gyara a tsarin ilimin makarantun Almajirai.

A cewar sarkin musulmin, gyara tsarin bada ilimi a makarantun tsangaya zai taimaka wajen farfaɗo da ɓangaren ilimi a Najeriya.

FG ta yaba da matakin gwamnatin Sokoto

A nata ɓangare, Maryam Uwais, mai baiwa shugaba Buhari shawara ta musamman kan ayyukan jin kai, ta yada da shirin gwamnatin Sokoto.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yan Bindigan dake tserowa daga luguden wutan Sojoji a Katsina da Zamfara sun fara shiga Kano

"Matasa da yara da dama, waɗanda ba su je makaranta ba, kuma basu da wata sana'a, suke taimakawa wajen ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya."

A wani labarin na daban kuma Buhari ya boye wa shugabannin duniya gaskiyar abinda ke faruwa a mulkinsa, Yan majalisa

Yan majalisar wakilai ƙarƙashin jam'iyyar adawa ta PDP, sun yi watsi da jawabin shugaba Buhari a wurin taron UNGA.

Yan majalisun sun bayyana cewa kalaman da shugaba Buhari ya gabatar ga shugabannin duniya ya yi hannun riga da gaskiyar abinda ke faruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel