Rikicin PDP: An kori shugabar mata, tsohon minista da wasu jiga-jigai a PDP

Rikicin PDP: An kori shugabar mata, tsohon minista da wasu jiga-jigai a PDP

  • Jam'iyyar PDP a jihar Kebbi ta yi kora da yawa na manyan jiga-jigan jam'iyyar a kasa da jihar
  • Rahoto ya bayyana cewa, an kori shugabar mata ta kasa na jam'iyyar bayan wata danbarwa
  • Rahoto kan batun bai gama cika ba, domin kuwa ba samu jin ta bakin mataimakin shugabn jam'iyyar na jihar Kebbi ba

Kebbi - Jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta kori tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Tanimu, wani Babban Lauyan Najeriya (SAN), da wasu mutane uku bisa zargin rashin da'a ga jam'iyya.

Mataimakin shugaban jam'iyyar ta PDP a shiyyar Kebbi ta tsakiya, Garba Abubakar Besse ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da Daily Trust ranar Lahadi 26 ga watan Satumba.

Ya ce sauran membobin da aka kora sune shugabar mata ta kasa na jam’iyyar, Hajiya Maria Umaru Waziri; shugaban jam'iyya na jihar, Haruna D. Sa’idu, da dan takarar gwamna na jam’iyyar a 2015, Janar Sarkin Yaki Bello (mai ritaya).

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Jam'iyyar PDP Ta Dakatar Da Jiga-Jiganta Biyu a Borno

Rikicin PDP: An kori shugabar mata, tsohon minista da wasu jiga-jigai a PDP
Jam'iyyar adawa ta PDP | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Ya ce an kore su daga jam'iyyar ne saboda mayar da sakateriyar jihar zuwa Abuja tare da yin awon gaba da fom din tsayawa takara na babban taron jam'iyyar da za a yi don amfanin masu biyayya ga jam'iyyar.

Da aka tuntubi Bello, ya ki cewa komai kan lamarin, yana mai cewa yana cikin wani taro. Wasu ba su amsa kiran da aka yi musu ba kuma ba su amsa sakonnin da aka aiko musu ba.

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu karbuwa a jam'iyyun siyasa 17 na kudanci

A wani ci gaba a PDP, shugabannin jam’iyyun siyasa 17 da kungiyoyin farar hula a jihar Delta a ranar Lahadin da ta gabata sun amince da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta sake dage babban taron jam'iyya na jihohi zuwa wani lokaci

Amincewar tana zuwa ne bayan bukatar gwamnoni jihohi 17 na kudancin kasar na neman shugaban kasa daga kudanci, Punch ta ruwaito. G

amayyar kungiyar Atiku Support Groups Initiative wacce ta sanar da amincewar ta yi ikirarin cewa bai kamata kabilanci ko bambancin siyasa su zama abin duba ga tsayar da dan takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Babban Darakta na ‘CASGI ATIKU 2023, Mista Obinna Okorie, ya fadi haka a lokacin kaddamar da kungiyar a garin Asaba.

Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP

A wani labarin daban, Daily Trust ta tabbatar da ficewar Sani daga hannun hadiminsa na kusa, Malam Suleiman Ahmed a makon jiya.

Ahmed ya ce mai gidan nasa ya sauya sheka ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, lokacin da yake ganawa da wasu jiga-jigan PDP a Kaduna. Shin me Sanata Sani zai samu da shiga jam'iyyar adawa ta PDP?

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP ta kori tsohon gwamnan Neja Aliyu a matsayin memba na BoT, ta sanar da madadin shi

A shekarar 2015, an zabi sanata Shehu Sani don wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki. Ya kasance mai sukar lamirin da kalubalantar lamurra da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.