Gwamnatin Buhari ta kashe N8.9tr a gina abubuwan more rayuwa a shekarar 2020

Gwamnatin Buhari ta kashe N8.9tr a gina abubuwan more rayuwa a shekarar 2020

  • Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da gidajen Dakkada a jihar Akwa Ibom
  • Mataimakin shugaban kasar ya yabi kokarin da gwamnan Akwa Ibom ya yi
  • Osinbajo yace gwamnatin APC ta kashe N8tr wajen abubuwan more rayuwa

Akwa Ibom - Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yace gwamnatin tarayya ta kashe Naira tiriliyan 8.9 wajen gina abubuwan more rayuwa a 2020.

Yemi Osinbajo ya bayyana haka wajen kaddamar da rukunin gidajen Dakkada luxury estate a Uyo, Akwa Ibom a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, 2021.

Farfesa Osinbajo yake cewa ba a taba yin gwamnatin da ta kashe kudi sosai domin samar da abubuwan more rayuwa ba irin ta Muhammadu Buhari.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa Osinbajo ya bayyana wasu ayyukan da gwamnatocin tarayya da na jiha suka yi a jihar ta Akwa Ibom daga 2015 zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Bamu kujeran shugaban kasa a 2023 ya zama wajibi, Afenifere ta jaddada bukatar kudu

Mataimakin shugaban kasar yace dogon Legas-Kalaba da aikin tashar ruwan Ibom da gidajen Dakkada da ake aiwatar wa sun gyara jihar Akwa Ibom.

Gwamnatin Buhari
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: govandbusinessjournal.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mun fi kowane gwamnati kokari - Osinbajo

“Tun da aka kafa gwamnatinmu, shugaban kasa ya maida hankali wajen samar da tituna, hanyoyin jiragen kasa, lantarki.”
“Duk da kalubalen tattalin da aka samu a shekaru shida, mun fi kowane gwamnati kokari gina abubuwan more rayuwa.”
“Zuwa shekarar da ta wuce, mun kashe fiye da Naira tiriliyan 8.9 wajen abubuwan more rayuwa. A watan da ya wuce majalisar FEC ta amince da aikin jirgin kasan Legas zuwa Kalaba wanda zai bi ta Uyo.”
“A karshen shekarar da ta wuce, majalisar FEC ta kuma amince da aikin tashar ruwan Ibom, bayan rokon da gwamna ya kawo.”

Rahoton yace Farfesa Osinbajo ya yabi gwamna Udom Emmanuel kan cika alkawarin da ya yi na gina gidajen Dakkada, wanda za su kawo wa jihar kudin-shiga.

Kara karanta wannan

Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu

Kwanakin baya aka ji Kakakin kungiyar dattawa, Arewa, Hakeem Baba Ahmed ya na cewa babu wanda ya isa ya yi masu dole a siyasa idan zaben 2023 ya zo.

Ralphs Okey Nwosu ya yi Allah-wadai da kalaman Dr. Hakeem Baba Ahmed. Shugaban jam’iyyar adawar, Ralphs Okey Nwosu ya fitar da jawabi a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel