Ku daina tsinewa shugabanninku saboda wahalar rayuwa – Sanusi ga ‘yan Najeriya

Ku daina tsinewa shugabanninku saboda wahalar rayuwa – Sanusi ga ‘yan Najeriya

  • Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su daina la’antar shugabanninsu saboda halin kunci da kasar ke ciki
  • Sanusi wanda ya kasance jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya ya ce Annabin tsira yana adawa da hakan
  • Ya kuma yi kira ga al'umman kasar da su hada kansu tare da guje ma duk abun da zai haddasa rashin zaman lafiya

Sokoto - Tsohon Sarkin Kano kuma jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya gargadi ‘yan Najeriya da su daina la’antar shugabanninsu saboda halin kunci da kasar ke ciki a yanzu.

Da yake jawabi ga mabiya Darikar daga jihohi bakwai na Arewa maso Yamma, a Sokoto a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, Sanusi ya bayyana kyakkyawan fata cewa abubuwa za su inganta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Ku daina tsinewa shugabanninku saboda wahalar rayuwa – Sanusi ga ‘yan Najeriya
Sanusi ya yi kira ga 'yan Najeriya da su daina tsinewa shugabanninsu saboda wahalar rayuwa Hoto: nairagent.com
Asali: UGC

Ya ce:

"A sanina game da tattalin arziki, na san cewa dole ne mu sha wahala don daidaita abubuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abin da ake so daga gare mu yanzu shine haƙuri, addu'o'i masu ƙarfi kuma dole ne mu tashi tsaye don inganta abubuwa da karfin iyawarmu ta hanyar halal.
"Dole ne mu guji cin zarafi ko la'antar shugabanninmu saboda Annabin tsira yana adawa da hakan.
“Kuma ba za mu saka kanmu cikin gurbatattun ayyuka da sauran miyagun ayyuka ba saboda addininmu yana wa’azi a kansa.
"Dole ne mu canza mu zama nagari sannan kuma mu kasance masu himma ga zaman lafiya da ci gaban al'ummomin mu.”

Sanusi ya kara tunatarwa kan hadin kan al'ummar musulmi sannan ya shawarci kungiyar musulmai da su kafa makarantu da shirye -shiryen karfafawa mabiyansu don dogaro da kai.

Ya jaddada cewa Musulunci ya kyamaci miyagun aiki, bara da sauran munanan dabi'u tare da karfafa hankali da mu'amala ta gaskiya.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Tsohon Sarkin ya yi kira ga mutane da su yi aiki da hakkokin addini daidai da koyarwar Musulunci.

Ya ja hankalinsu game da guje ma batutuwan da za su raba kan al'umma.

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II, Ya Magantu Kan Kudirin FG Na Zare Tallafin Man Fetur da Wutar Lantarki

A wani labari na daban, tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya yi kira ga yan Najeriya su shirya su fara tunanin abinda zasu yi domin tallafa wa kansu maimakon dora komai kan gwamnati.

Sanusi, wanda shine khalifan tijjaniyya a Najeriya, ya faɗi haka ne a wurin taron bikin da aka shirya domin murnar cikarsa shekara 60 a duniya.

Tsohon sarkin yace: "Ya kamata yan Najeriya su fahimci cewa hanyar da muka biyo ba mai ɓullewa bace. Ba zai yiwu gwamnati ta cigaba da biyan tallafin fetur ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel