Tsohon Shugaban INEC, Jega ya bada shawarar a kashe Jihohi 24 a Najeriya, a bar Gwamnoni 12

Tsohon Shugaban INEC, Jega ya bada shawarar a kashe Jihohi 24 a Najeriya, a bar Gwamnoni 12

Farfesa Attahiru Jega ya soki kiran a kirkiro wasu sababbin jihohi a Najeriya

Tsohon shugaban hukumar INEC ya bada shawarar a koma tsarin jihohi 12

Jega yana ganin tara jihohi barkatai ba zai kawo karshen kukan da aka yi ba

Abuja - Tsohon shugaban hukumar gudanar da zabe na kasa, Attahiru Jega, ya yi kira cewa a rage adadin jihohin da ke kasar nan domin a iya samun cigaba.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa da yake magana a garin Abuja, Attahiru Jega ya bada shawarar a soke jihohi 24, ta yadda za a zauna da jihohi 12.

Farfesan ya yi wannan jawabi ranar Talata, 21 ga watan Satumba, 2021 wajen kaddamar da tafiyar Rescue Nigeria Project wanda shi da wasu suka shigo da ita.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta sake dage babban taron jam'iyya na jihohi zuwa wani lokaci

Jega ya kawo wannan shawara ganin yadda ‘yan siyasa suke rashin adalci da facaka da dukiyar mutane, yace marasa kan gano aka bari suna jagorancin kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jihohi 12 suka dace

“A wargaza tsarin jihohi 36, a koma wa yadda ake kai kafin 1966 na tsarin yankuna, ko na shiyyoyi shida ko kuma ma tsarin jihohi 12 da aka yi a 1976/77.”

A cewar Jega wanda ya rike INEC tsakanin 2010 zuwa 2015, hakan ne ya fi dace wa da Najeriya.

Tsohon Shugaban INEC
Attahiru Jega Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Ina maganar kirkiro wasu jihohin?

Kamar yadda aka kawo rahoto, Farfesa Jega ba ya tare da masu cewa a kirkiro wasu jihohi, yace hakan ba zai magance matsalolin da suke damun al’umma ba.

“Kara kirkiro jihohi 42 daga 36 da ake da su ba abu ne mai bulle wa ba, kanzon kurege ne, za dai a iya fada, amma ba zai yiwu a iya aiwatar da shi a aikace ba.”

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Matsalolin yin hakan ya zarce amfaninsa nesa ba kusa ba. Iya adadin jihohin da aka kirkira, iya kalubalen tattalin, wasu kuma za su rika kukan ana cutarsu.”

Idan za ayi wa tsarin kasa garambawul na hakika, Farfesan ya bada shawarar gwamnatin tarayya ta raba dukiyar kasa ne tare da sauran bangarorin gwamnati.

Najeriya za ta ci bashin $4bn

A ranar Talata aka ji cewa ‘Yan Majalisar Dattawa za su fara zama a kan rokon sabon bashin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar wa Sanatocin kwanaki.

Duk da ana bin Najeriya bashin N35tr, ana neman sake karbo aron N2tr daga kasashen waje. Gwamnatin tarayya tace za a yi wa al'umma ayyuka ne da bashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel