Lokuta 5 da Zulum ya kai ziyarar bazata ma'aikatu a jihar Borno kuma ya bada mamaki
Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno ya fita daban cikin sauran takwarorinsa wajen nuna kwarewa tabbatar da ma'aikatan jiharsa na aiki kamar yadda ya kamata.
Lokaci bayan lokaci, gwamnan ya kan kai ziyarar bazata makarantu ko asibitoci ko ma'aikatu domin ganin halin da ma'aikatan ke ciki.
A wadannan lokuta, gwmanan ya ladabtar da ma'aikatan da suke kin zama a bakin aikinsu duk da suna karban albashi.
Ga jerin lokutan da gwamnan ya kai ziyarar bazata kuma ya bada mamaki:
1. Yuli 2019: Zulum ya kai ziyara Asibiti cikin dare, ya tarar babu likita ko guda
A ranar 31 ga Yuli, watanni biyu da hawa mulkinsa, gwamna Zulum ya ziyara asibitin Umaru Shehu cikin dare inda ya tarar babu Likita ko guda.
Bugun farko Gwamnan ya fara da ziyarar a asibitin Umaru Shehu inda ya tarar babu wani Kwararren likita da ke bakin aiki a asibitin cikin karrarun likitoci 10 da suke aiki a asibitin
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A lokacin da ya tarar da ma'akatan jinya guda 10 cikin 138 dake aiki a asibitin. Nan take Gwamnan ya kira duka Likitoci goma da suke aiki a asibitin ta waya amma bai same su ba.
Daga karshe Gwamnan ya garzaya Asibitin Kwararru na jihar inda can ma ya tarar da wasu Likitoci ba sa bakin aiki.
2. Zulum ya kai ziyara makaranta da asuba
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya jinjina wa wata malamar makarantar firamare dake jihar bisa maida hankali da tayi a wajen aikin ta na malunta.
Wannan malama wacce ‘yar asalin jihar Abia ce ta shekara 31 tana karantarwa a makarantar firamare na Kyarimi da ke Maiduguri.
Ko da gwamna Zulum ya kai ziyarar bazata wannan makaranta da misalin karfe 6:30 na safe, sai ya iske babu kowa a makarantar, babu malami, ko dalibi ko da guda daya ne kuwa.
Amma kuma abin mamaki sai ya iske wata malama ita kadai tilo ta na zaune tana jiran dalibai.
3. Gwamna Zulum ya yiwa wani likita Bayarbe kyautar mota da biyansa kudi N13.9m
A ranar 13 ga Febrairu 2021, Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da biyan naira miliyan 13.9 da kyautar mota ga wani likita mai shekaru 65 daga jihar Ogun.
Likitan shine wanda ke zaune a cikin Babban Asibitin da ke Monguno kuma ya ci gaba da kula da marasa lafiya har ma lokacin da garin ya fuskanci mummunar barazanar kungiyar Boko Haram.
Zulum ya bayyana cewa Dr. Isa Akinbode ya kwashe shekaru 22 yana aiki a jihar Borno kafin yayi ritaya a 2016 a Asibitin Monguno.
Bayan ritayarsa, Likitan da Boko Haram suka taba sacewa a Monguno ya cigaba da aiki kyauta.
4. Farfesa Zulum ya shiga aji kwatsam, ya yi wa Malamai gwaji domin ya auna kaifin basirarsu
A ranar Litinin, 9 ga Agusta, 2021, mai girma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya shirya wata jarrabawar ba-zata ga malaman makaranta a garin Baga.
Kamar yadda hadimin gwamnan, Isa Gusau ya fada, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi hakan ne domin ya gane ilmi da kwarewar wadannan malamai.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce bai yi wannan jarrabawa da nufin ya kori wani malami daga aki ba, sai dai domin sanin inda ya kamata a tura su.
5. Gwamna Zulum ya dakatar da shugabannin makarantar da ya yi karatu yayin da ya kai ziyarar bazata
Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da dukkanin shugabannin kwalejin kimiyya ta Ramat da ke Maiduguri, na tsawon watanni shida.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Zulum ya kasance dalibin kwalejin kimiyyar daga shekarar 1986 zuwa 1988.
A yayin ziyarar bazata da ya kai, gwamnan ya yi mamakin ganin cewa dakunan bitar aiki da na gwaje-gwaje ba sa aiki, yayin da ‘makarantar ta mutu murus’.
Asali: Legit.ng