An rufe bankuna a jihar Ogun bayan 'yan fashi sun yi barazanar kai farmaki
- Bankunan da ke Ijebu- Ode a jihar Ogun sun rufe saboda tsoron ka ‘yan fashi su kai mu su farmaki
- Tuni rahotanni sun bayyana yadda shaguna suka garkame tare da daina aiki tun ranar Litinin a jihar
- Wannan ya biyo bayan wasiku da ake zargin wasu ‘yan fashi da makamai suka tura yankunan
Ogun - Bankunan da ke Ijebu-Ode a jihar Ogun sun rufe sakamakon tsoron kada masu fashi da makamai su kai mu su farmaki.
Daily Trust ta ruwaito yadda masu shaguna suka rufe tun Litinin da safe bayan wasu wasiku da wasu da ake zargin ‘yan fashi suka tura wa wasun su.
Lamarin ya tsorata mazauna yankin yayin da abokan huldar bankunan suka shiga damuwa suka tsaya bakin bankunan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Majiya daga bankuna sun bayyana cewa ba za su koma ba har sai gwamnatin jihar ta taimaka mu su da ‘yan sanda masu makamai don kulawa da su.
Mazauna yankin Ijebu-Ode kuwa sun nufi garuruwa kamar Sagamu, Abeokuta da sauran su don ciro, Daily Trust ta wallafa.
Wani mai POS kuwa mai suna Salim ya bayyana cewa da za su yi amfani da damar wurin samun kudi a anguwar amma hakan ba zai yuwu ba.
Kamar yadda ya ce:
“Muna debo kudi daga bankuna sannan muna amsar kudi masu yawa daga hannun su mu kai banki. Idan bankuna ba sa budewa mu ma za mu cutu. Yanzu haka ma mun takura, ina ta zuwa Sagamu ina ciro kudi.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemu ya ce babu wani dalilin tsoron kada su kai farmaki, ya tabbatar wa da bankuna cewa babu wata matsala kuma mazauna yankin su kwantar da hankulan su.
Kamar yadda ya ce:
“Babu wani abin ban tsoro; ko DPO din yankin ya ce kada su tsorata. Saboda me za su tsorata ko don babu jami’ai masu makamai? Ko da ba sa aiki akwai ‘yan sandan da suke aiki.
“Yan sanda za su tabbatar sun kula da lafiya da dukiyoyin jama’a. Mun tabbatar mu su da cewa za mu kare martabar su da dukiyoyin duk mazauna Ijebu-Ode da ke jihar Ogun. Babu dalilin tsorata.”
Ba za mu sakankance bakin haure su mamaye Najeriya ba, Rundunar sojin kasa
A wani labari na daban, kwamandan rundunar hadin guiwa ta Operation Hadin Kai, Maj.-Gen. Christopher Musa, ya ce dakarun sojin Najeriya ba za su bar kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta samu wuri tare da yin kane-kane a Najeriya ba.
Musa ya sanar da hakan ne yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.
Kamar yadda ya ce, ISWAP kungiyar ta'addanci ce ta ketare wacce wasu daga kasashen ketaren ke daukar nauyin ta, ta yuwu kuma akwai wasu 'yan Najeriya da ke daukar nauyin ta. Don haka ba ta da wurin zama a kasar nan.
Asali: Legit.ng