Bidiyon NYSC na shawarta masu hidimar kasa su tattara kudin fansarsu da kansu

Bidiyon NYSC na shawarta masu hidimar kasa su tattara kudin fansarsu da kansu

  • Jama'a sun yi caa a kan hukumar NYSC bayan wata shawarar da ta bai wa masu hidimar kasa ta bayyana
  • NYSC ta bukaci masu hidimar kasa da su sanar da iyayensu da 'yan uwa domin biyan kudin fansa idan an sace su a tituna masu hatsari
  • Duk da yana rubuce a littafin shawarar tsaro na hukumar, NYSC ta musanta tare da cewa kage masu son tada zaune tsaye suka musu

A halin yanzu hukumar NYSC ta shiga wani rudani sakamakon wani cece-kuce kan dokokin tsaro da suka bai wa matasa masu hidimar kasa, Daily Trust ta wallafa.

A wani littafi mai suna “Security Awareness and Education Handbook For Corps Members and Staff'” NYSC ta bayyana manyan titunan Abuja zuwa Kaduna, Abuja zuwa Lokoja zuwa Okene da Aba zuwa Fatakwal daga cikin tituna masu tsananin hatsari.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Bidiyon NYSC na shawarta masu hidimar kasa su tattara kudin fansarsu da kansu
Bidiyon NYSC na shawarta masu hidimar kasa su tattara kudin fansarsu da kansu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A shafi na 56 na littafin, an shawarci matasa masu kaiwa da kawowa kan wadannan titunan da su sanar da 'yan uwansu tare da samun wanda zai biya kudin fansa matukar aka yi garkuwa da su.

An rabawa matasa masu hidimar kasa kashi na biyu ne wannan littafin, Daily Trust ta wallafa.

Babu shakka wannan shawarar ta janyo cece-kuce da kushe a kafafen sada zumuntar zamani saboda jama'a da dama na cewa alama ce da ke nuna cewa Najeriya ta gaza.

NYSC ta musanta

Sai dai, a wata takarda da NYSC ta saki ranar Juma'a, ta kwatanta labarin da na kanzon kurege kuma tsabar kage ce aka mata domin ba ta bada wannan shawarar ba.

"Hankalin hukumar NYSC ya kai kan wata wallafar kage da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani kan matasan da ke hidimar kasa masu kaiwa da kawowa kan tituna masu hatsari da su sanar da 'yan uwansu domin biyan kudin fansa idan an sace su."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bincike ya nuna abinda ya kashe budurwar da aka tsinci gawarta cikin motar basarake da ya tsere

“Hukumar ta na son tabbatar da cewa wannan ba ya cikin ladubban tsaro na su wanda kwararru a harkar tsaro suke hadawa.
“Hukumar na kira ga jama'a da su tabbatar sun tantance duk wani abu da zai fito daga hukumar. Kada a fada tarkon 'yan gangan da ke hada labarai domin bata sunan hukumar.
“Hukumar za ta cigaba da fifita tsaro da kuma jin dadin masu hidimar kasa da ma'aikatan ta a kowanne lokaci," takardar tace.

Rundunar soji: Muna mutunta su ne kawai, ba tarairayar tubabbun 'yan ta'adda mu ke ba

A wani labari na daban, Christopher Musa kwamandan rundunar hadin guiwa ta arewa maso gabas, operation Hadin Kai, ya ce rundunar soja ba ta tarairaya da yi wa tubabbun 'yan ta'adda gata, TheCable ta ruwaito.

A yayin jawabi a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, Musa ya ce hukuncin barin 'yan ta'adda su mika wuya ga sojoji lamari ne da yayi daidai da dokokin kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Kaduna: Hotunan 'yan sanda masu murabus suna yi wa hukumar fansho zanga-zanga

Ya ce idan makiyi ya mika wuya yayin yaki, ba a amince sojoji ko mayakan su harbi wannan makiyin ba. Ya ce dole ne rundunar ta dinga mu'amala da su kamar yadda za ta yi da mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng