Jam'iyyar APC ta bayyana dalilin da yasa ta dage gangamin taronta na jihohi

Jam'iyyar APC ta bayyana dalilin da yasa ta dage gangamin taronta na jihohi

  • Jam'iyya mai mulkin ƙsar nan APC, ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ɗage gangamin jihohi ne saboda bikin ranar samun yancin kai
  • APC tace ranar da ta saka da farko, ta kasance kwana ɗaya tal bayan ranar bikin samun yankin kai, kuma mambobinta zasu halarci bikin a jihohinsu
  • Sai dai wasu majoyoyi masu karfi sun bayyana cewa APC ta ɗage taron ne saboda ɓarakar dake neman kunno kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyya

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa ta ɗage gangamin tarukanta na jihohi daga 2 ga watan Oktoba zuwa 16 ga watan Oktoba, 2021, saboda cikar Najeriya shekara 61 da samun yancin kai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Jam'iyyar ta faɗi haka ne a wani jawabi da ta fitar ranar Alhamis, ɗauke da sa hannun sakataren kwamitin rikon kwarya na APC, sanata John James Akpanudoedehe.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta sake dage babban taron jam'iyya na jihohi zuwa wani lokaci

Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC ta bayyana dalilin da yasa ta dage gangamin taronta na jihohi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A jawabin da sakataren ya fitar, APC tace:

"Saboda mu girmama bikin cikar Najeriya shekara 61 da samun yancin kai, wanda za'a yi kwana ɗaya kafin ranar taron da muka sanya da farko, shiyasa muka sanar da sabon lokaci."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamnoni, ministoci da sauran mambobin jam'iyya zasu gudanar da bikin yancin kai a ranar a jihohinsu."
"Jam'iyya ta yanke hukuncin canza ranar gangamin taron jihohi domin baiwa mambobin jam'iyya damar halartar bikin samun yancin kai a garuruwansu."

An ya kuwa dalilin ɗage tarukan APC kenan?

A ranar Laraba, Sanata James Akpanudoedehe, ya bayyana cewa ba da jimawa jam'iyya zata fitar da sabon jadawalin yadda tarukan zasu gudana, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa APC ta ɗage ranar ne domin samun damar yin sulhu a jihohi don gujewa rikici da kuma warware sakamakon zaɓukan da za'a gudanar.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Jihohin Arewa 7 sun hada kai zasu ɗauki jami'an tsaro 3,000, Masari

Wane irin rikici APC take gudu?

Wata majiya tace:

"Sun shiga ruɗani ne, domin rikicin da ka iya faruwa zai iya yin awon gaba da kashi 60 da mambobin jam'iyyar APC. Ni kaina zan iya ficewa daga APC."
"Sun hangi abinda ke faruwa shiyasa suka ɗage gangamin zaɓukan jihohi domin a ɗinke duk wata ɓaraka da ta kunno kai."

A wani labarin kuma Asirin Miyagun da suka sace dalibai a makarantar Bethel Baptist Kaduna ya tonu

Gwarazan jami'an rundunar yan sandan ƙasar nan sun samu nasarar damƙe mutum uku daga cikin yan bindigan da suka sace ɗaliban Bethel Baptist Kaduna.

Mutanen da ake zargin, sun amsa laifinsu kuma sun bayyana cewa su 25 ne suka kai hari makarantar dake Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262