Da Ɗumi-Dumi: Asirin Miyagun da suka sace dalibai a makarantar Bethel Baptist Kaduna ya tonu
- Gwarazan jami'an rundunar yan sandan ƙasar nan sun samu nasarar damƙe mutum uku daga cikin yan bindigan da suka sace ɗaliban Bethel Baptist Kaduna
- Mutanen da ake zargin, sun amsa laifinsu kuma sun bayyana cewa su 25 ne suka kai hari makarantar dake Kaduna
- Ɗaya daga cikinsu, ya shaidawa manema labarai cewa, sun yi garkuwa da ɗaliban ne domin su samu kuɗi
Kaduna - Gwarazan jami'an rundunar yan sanda sun cafke mutum uku daga cikin miyagun yan bindigan da suka sace ɗalibai sama da 100 a Bethel Baptist Kaduna, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Kakakin rundunar yan sanda ta ƙasa, Frank Mba, ya jera mutanen da ake zargin, waɗanda suka saka kakin sojoji, a hedkwatar rundunar SARS, a Abuja.
Mutanen guda uku da jami'an yan sanda suka samu nasarar cafke wa, sun amsa laifinsu cewa suna da hannu a garkuwa da ɗaliban.
Meyasa suka sace ɗaliban Bethel Baptist?
Waɗanda ake zargin, Adamu Bello, Isiaku Lawal da kuma Muazu Abubakar, sun shaidawa manema labarai cewa su 25 ne suka sace ɗaliban makarantar.
Mutanen uku sun ƙara da cewa sun aikata garkuwa da ɗaliban ne a ƙoƙarinsu ma samun kuɗi ta kowace hanya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ɗaya daga cikinsu, Muazu Abubakar, ɗan kimanin shekara 27 a duniya, yace:
"Mu 25 ne muka kai hari makarantar, mun yi garkuwa da ɗalibai 136 kuma na samu dubu N100,000 kaso na daga cikin kuɗin fansar da muka samu."
A wani labarin na daban Kotu ta sanar da ranar yanke hukunci kan shari'ar tsohon sarkin Kano, Sanusi II, da Gwamnatin Kano
Kotun tarayya dake zaman a babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana ranar da zata yanke hukunci kan karar da tsohon sarkin Kano ya shigar.
Tun bayan sauke shi daga mukamin sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya shigar da gwamnatin kano ƙara da wasu manyan mutane a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng