Jam'iyyar APC ta sake dage babban taron jam'iyya na jihohi zuwa wani lokaci

Jam'iyyar APC ta sake dage babban taron jam'iyya na jihohi zuwa wani lokaci

  • Jam'iyyar APC ta bayyana dage taron ta na jihohi zuwa wani lokaci nan kusa; makwanni biyu
  • A baya jam'iyyar ta APC ta sanya ranar 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar manyan tarukan jihohi
  • Zuwa lokacin hada wannan rahoto, APC ba ta ambaci dalilin dage wannan taro na jihohi ba

Jam'iyyar APC mai mulki ta sake dage zaman Babban Taron majalisar jam'iyya na jihohi zuwa wasu makwanni biyu.

An fara shirin taron wanda aka shirya yi ranar 2 ga Oktoba, 2021, yanzu kuma ya koma 16 ga Oktoba, 2021.

Yanzu-Yanzu: APC ta sake dage taron gangaminta na jihohi
Jam'iyyar APC ta dage taron jihohi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A ranar Laraba, Sakataren Kwamitin Tsare-Tsare na babban taro na APC, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce za a fitar da sabon jadawali/tsarin ayyuka da jagororin gudanar da taron ga jama'a a kan kari.

Kara karanta wannan

Gwamnan Neja ya dakatad da zaben sabon Sarkin Kontagoran kan zargin murdiya

Kokarin da wakilin Daily Trust ya yi don gano dalilin da ya sa aka dage taron bai samu nasara ba a lokacin hada wannan rahoton.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasa a 2023: Kudu ba za ta goyi bayan duk jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa ba, in ji gwamnan APC

Gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, ya ce duk wata jam’iyyar siyasa da ta tsayar da dan takarar arewa a matsayin shugaban kasa a 2023 na iya rasa goyon bayan mutanen kudu.

Akeredolu ya bayyana haka ne ranar Juma’a a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels da TheCable ke sa ido.

A yayin da yake magana kan kudurin kungiyar gwamnonin kudancin kasar kan zabukan 2023 da kuma cewa dole ne a bai wa yankin kudu shugabancin kasa, Akeredolu, wanda shi ne shugaban kungiyar, ya ce hakan ta kasance ne domin a yi adalci da daidaito.

Kara karanta wannan

Yadda akayi jana'izar Sarkin Rano, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, ta gudana

Ya yi ikirarin cewa lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan Arewa, ya kammala wa’adin sa na biyu a 2023, yakamata shugaban kasa ya fito daga Kudu, jaridar Punch ta ruwaito.

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu karbuwa a jam'iyyun siyasa 17 na kudanci

A wani labarin, Shugabannin jam’iyyun siyasa 17 da kungiyoyin farar hula a jihar Delta a ranar Lahadin da ta gabata sun amince da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Amincewar tana zuwa ne bayan bukatar gwamnoni jihohi 17 na kudancin kasar na neman shugaban kasa daga kudanci, Punch ta ruwaito.

Gamayyar kungiyar Atiku Support Groups Initiative wacce ta sanar da amincewar ta yi ikirarin cewa bai kamata kabilanci ko bambancin siyasa su zama abin duba ga tsayar da dan takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.