Yanzu Yanzu: Bayan rasuwar mahaifinsa, Gwamnan Najeriya ya sake shiga alhinin rashi

Yanzu Yanzu: Bayan rasuwar mahaifinsa, Gwamnan Najeriya ya sake shiga alhinin rashi

  • Gwamnatin jihar Delta baki daya ta fada cikin jimamin mutuwar Mary Iyasere
  • Har zuwa mutuwarta, Iyasere ita ce mai ba da shawara na musamman ga Gwamna Ifeanyi Okowa kan bunƙasa harkokin kasuwanci
  • Iyasere ta taba zama kwamishinar kasuwanci da yawon bude ido a lokacin mulkin gwamnan na farko

Delta - Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, ya rasa mai ba shi shawara na musamman kan ci gaban kasuwanci, Mary Iyasere.

Daga baya Marigayiya Iyasere wacce ta yi aiki a matsayin kwamishinar kasuwanci da yawon shakatawa na jihar a lokacin gwamnatin Gwamna Okowa na farko, ta koma kan mukamin da take kai har zuwa mutuwarta, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ku mamaye titunan Abuja, Kungiyar Ohanaeze Worldwide ga IPOB

Yanzu-yanzu: Bayan rasuwar mahaifinsa, Gwamnan Najeriya ya sake shiga alhinin rashi
Gwamnan Ifeanyi Okowa ya rasa hadimarsa Hoto: Governor Ifeanyi Okowa
Asali: Facebook

A zahiri, mutuwar Iyasere ta kawo baƙin ciki ga ubangidanta, membobin majalisarsa, da gwamnatin jihar.

Marigayiyar lauyar wacce ta fito daga garin Urhuakpor, ta kasance cif ta Urhobo a masarautar Agbon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wataƙila za a fi tunawa da ita kasancewar ita ce ta kafa kungiyar Urhuakpor Women in Politics (UWIP) ta karamar hukumar Ethiope East.

Mahaifin Gwamna Okowa, Okorie Okowa ya mutu

Idan za ku tuna, Mahaifin Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, Cif Arthur Okorie Uzoma ya riga mu gidan gaskiya, a safiyar ranar Alhamis, 28 ga watan Janairu.

Ya rasu ne bayan shafe shekaru 88 a doron kasa. Mahaifin gwamnan da ya fito daga Owa-Alero a karamar hukumar Ika North East na jihar ya rasu ne a babban birnin jihar wato Asaba.

Kafin rasuwarsa, marigayi Cif Arthur Okorie Uzoma wanda ake yi wa lakabi da AOU shine ke rike da sarautar Okpara-Uku na Owa-Alero.

Kara karanta wannan

Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu

Wani majiya daga iyalansa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa dattijon ya dade yana rashin lafiya kuma ya samu sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng