Da duminsa: Mahaifin Gwamna Okowa, Okorie Okowa ya mutu

Da duminsa: Mahaifin Gwamna Okowa, Okorie Okowa ya mutu

- Cif Arthur Okorie Uzoma, mahaifin gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya rasu

- Marigayin ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis 28 ga watan Janairu a Asaba, babban birnin jihar Delta

- Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da rasuwarsa sannan ta ce ya dade yana fama da rashin lafiya yana samun sauki

Mahaifin Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, Cif Arthur Okorie Uzoma ya riga mu gidan gaskiya, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis bayan shafe shekaru 88 a doron kasa. Mahaifin gwamnan da ya fito daga Owa-Alero a karamar hukumar Ika North East na jihar ya rasu ne a babban birnin jihar wato Asaba.

Da duminsa: Mahaifin Gwamna Okowa, Okorie Okowa ya mutu
Da duminsa: Mahaifin Gwamna Okowa, Okorie Okowa ya mutu. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kuɗin ɗawainiyar jana'izar mahaifina na ke nema, matashin da aka kama da katin ATM 17

Kafin rasuwarsa, marigayi Cif Arthur Okorie Uzoma wanda ake yi wa lakabi da AOU shine ke rike da sarautar Okpara-Uku na Owa-Alero.

Wani majiya daga iyalansa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa dattijon ya dade yana rashin lafiya kuma ya samu sauki.

KU KARANTA: Kungiyar tsaffin dalibai na MSS sun nuna kin amincewarsu kan yunkurin rushe masallacin makaranta a Binuwai

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a sanar da abinda ya yi sanadin rasuwarsa ba.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: