Mai shekaru 52 ya dirkawa 'yar dan uwansa mai shekaru 16 ciki har sau biyu

Mai shekaru 52 ya dirkawa 'yar dan uwansa mai shekaru 16 ciki har sau biyu

  • 'Yan sanda sun cafke wani mutum da laifin yi wa 'yar da uwansa ciki har sau biyu tare da zubarwa
  • Bayan gudanar da bincike, mutumin ya amsa laifinsa, ya kuma bayyana yadda aka yi ya zubar da cikin
  • Rundunar 'yan sanda ta shawarci iyaye kan su kula da 'ya'yansu mata a irin wannan yanayi da ake ciki

Ogun - Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta cafke wani mutum mai shekaru 52, Jimoh Mutaliu, saboda yi wa diyar 'yar uwarsa mai shekara 16 ciki har sau biyu sannan ya zubar mata da cikin.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, a ranar Laraba 22 ga watan Satumba a Ota ta jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

DSP Oyeyemi ya ce an cafke wanda ake zargin ne a ranar 21 ga watan Satumba, bayan rahoton da mahaifin mamacin ya kai a ofishin ‘yan sanda na Adatan cewa‘ yarsa mai shekara 16 tana da ciki.

Kara karanta wannan

Baki kan yanka wuya: An yanke wa Hassan shekaru 2 a gidan yari saboda ya kira ‘yan sanda ɓarayi a Adamawa

Mai shekaru 52 ya dirkawa 'yar dan uwansa mai shekaru 16 ciki har sau biyu
'Yan sandan Najeriya | Hoto: cms.qz.com
Asali: UGC

DSP Oyeyemi ya ce:

“Mahaifin wacce abin ya rutsa da ita ya yi zargin cewa dan uwansa ne ke da alhakin yin cikin, yana mai cewa ya jima yana kwanciya da ita kuma ya zubar mata da ciki biyu.
"Bayan samun rahoton, 'yan sanda sun cafke wanda ake zargi kuma a yayin da ake yi masa tambayoyi, ya yi bayanin ikirarin cewa da gaske ya aikata laifin.
"Ya kuma tabbatar da cewa ya zubar mata da ciki har sau biyu da taimakon wata ma'aikaciyar jinya."

Kakakin 'yan sandan ya nuna damuwar sa kan yawan mace-macen mata a jihar sannan ya shawarci iyaye mata da su kula da 'ya'yan su mata.

Wata budurwa ta bakunci lahira yayin da take lalata da saurayinta a mota

Mutuwa ta dauke wata budurwa mai suna Gabrielly Dickson a yayin da suke tsaka da fasikanci da saurayinta mai shekaru 26 a cikin mota.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane

An garzaya da budurwar mai shekara 15 zuwa asibiti ne bayan saurayin nata da yake fasikanci da ita ya lura cewa ta fita daga hayyacinta, in ji Aminiya.

’Yan sanda da ke binciken lamarin sun ce saurayin, wanda ake kira “babban mai taimako”, ya shaida musu cewa yana cikin saduwa da ita a cikin mota ne ya lura labbanta da fatar jikinta sun koma fari fat, hannuwanta kuma sun jujjuye.

Ko da aka kai ta asibiti, likitoci sun gano zuciyarta ta buga, amma babu yadda suka iya, washegari da safe kuma ta sheka lahira.

Wani kamfani zai biya makudan kudade ga mai son ya kalli wasu fina-finai 13

A wani labarin, akan kalli fina-finai domin nishadi da debe kewa, hakazalika da ma bata lokacin zama ba aikin komai, amma kun taba tunanin akwai fim din da zaku kalla kuma a biya ku kudade?

Wani kamfanin hada-hadar kudi zai ba da $1,300 (N534,950.00) ga duk wanda ke son zama ya kalli wasu manyan fina-finai masu ban tsoro da aka taba yi a duniya.

Kara karanta wannan

IGP Ga Jami'an Yan Sanda: Aikin Ku Zai Iya Jefa Ku Wuta Ko Aljanna Ranar Gobe Ƙiyama

A cewar CNN, kamfanin mai suna FinanceBuzz yana bincike ne don sanin ko girman kasafin kudin fina-finan yana tasiri da yadda tasirinsa yake ga masu kallo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.