Wani kamfani zai biya makudan kudade ga mai son ya kalli wasu fina-finai 13
- Wani kamfanin hada-hadar kudi zai dauki nauyin wani bincike mai ban sha'awa ga masu kallon fina-finai
- A wannan karo, ana son burge masu kallon fina-finan ban tsaro ta hanyar gudanar da wani bincike
- Ana bukatar mutum ya kalli wasu fina-finai sannan a biya shi makudan kudade cikin kankanin lokaci
Akan kalli fina-finai domin nishadi da debe kewa, hakazalika da ma bata lokacin zama ba aikin komai, amma kun taba tunanin akwai fim din da zaku kalla kuma a biya ku kudade?
Wani kamfanin hada-hadar kudi zai ba da $1,300 (N534,950.00) ga duk wanda ke son zama ya kalli wasu manyan fina-finai masu ban tsoro da aka taba yi a duniya.
Manufar yin haka
A cewar CNN, kamfanin mai suna FinanceBuzz yana bincike ne don sanin ko girman kasafin kudin fina-finan yana tasiri da yadda tasirinsa yake ga masu kallo.
Kamfanin zai yi hayar wani don ya zama mai yin duba da lura kan bugun zuciya, kuma yayin da mutum ke kallon fina-finan, za a kula da bugun zuciyarsa ta amfani da na'urar Fitbit don gano wasu abubuwa.
Jerin sunayen fina-finan
Wasu daga cikin sunayen fina-finan na sanya mutum mai saurin tsorata shiga wani yanayi na tsoro.
Ga fina-finan kamar haka:
- Get Out
- Halloween(2018)
- Saw
- A Quiet Place
- Insidious
- Amityville Horror
- A Quiet Place Part 2
- The Purge
- Candyman
- The Blair Witch Project
- Annabelle
- Sinister
- Paranormal Activity
Yadda za a shiga tsarin
Za a bubaci duk wanda aka zaba ya kalli fina-finan 13 tsakanin 9 ga Oktoba zuwa 18 ga Oktoba.
Kamfanin zai bai wa manazarcin da zai kula da shirin na'urar Fitbit, kudaden lada da kuma wasu karin $50 (N20,575).
Domin shiga shirin, ana bukatar mai sha'awa ya cike fom kuma ya gaya wa kamfanin dalilin da yasa yake ganin shi ne mafi cancanta a wannan shiri.
Za a gama cike fom din a ranar 26 ga watan Satumba, za a bayyana sunan wanda ya ci nasara a ranar 1 ga watan Oktoba.
Kamfanin iPhone ya kera iPhone 13 Pro Max, wayar da ba a taba irinta ba a fasaha
A wani labarin, Babban kamfanin fasaha na Apple ya sanar da kirkirar sabuwar waya mai suna iPhone 13 Pro, irinta na farko wanda ke ba da ma'ajiyar bayanai Terabyte daya (1TB), yana bawa masu amfani da iPhone damar adana bayanai kwatankwacin na iPhone 13 sau biyu.
An sanar da sabon samfurin yayin taron yanar gizo da kamfanin a ranar Talata 14 ga watan Satumba, in ji rahotom Peoples Gazette.
Kodayake kamfanin fasahar a baya ya daura ma'ajiyar bayanai 1TB a kan iPad, samfuran iPhone suna da adadin ajiyar da a kai 512GB.
Asali: Legit.ng