Baki kan yanka wuya: An yanke wa Hassan shekaru 2 a gidan yari saboda ya kira ‘yan sanda ɓarayi a Adamawa

Baki kan yanka wuya: An yanke wa Hassan shekaru 2 a gidan yari saboda ya kira ‘yan sanda ɓarayi a Adamawa

  • Kotu ta yanke wa Bala Hassan mai shekaru 25 hukuncin shekaru 2 a gidan gyaran hali saboda ya kira ‘yan sanda da barayi
  • An yanke masa hukuncin ne a ranar 21 ga watan Satumba sannan an kama shi da wani busasshen ganye da ake zargin wiwi ne
  • Bayan ‘yan sandan sintiri sun kai shi ofishin su don bincike akan ganyen, bai yi kasa a guiwa ba ya yi ta zagin su yadda ya ga dama

Jihar Adamawa - Kotu ta yanke wa wani Bala Hassan mai shekaru 25 daurin shekaru 2 a gidan gyaran hali bayan ya kira ‘yan sanda da barayi.

An yanke masa hukuncin a ranar 21 ga watan Satumba bayan kotun masu laifi ta Yola ta 2 ta yi shari’a kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane

Baki kan yanka wuya: An yanke wa Hassan shekaru 2 a gidan yari saboda ya kira ‘yan sanda ɓarayi a Adamawa
Bala Hassan da aka yanke wa hukunci kan kiran 'yan sanda barayi. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Dama an kama shi da wani ganye da ake zargin wiwi ne

Takardun kotu sun bayyana cewa an kama Bala a ranar Litinin 19 ga watan Satumba ne yayin wani sintiri da sifeta Ishaya Buba na ofishin ‘yan sandan Jimeta ya jagoranta. An ga wani busasshen ganye a hannun sa da ake zargin wiwi ne.

Bayan kai shi ofishin ‘yan sandan ya zurfafa bincike, ya ki yin bayani mai kyau sannan ya hau zagin ‘yan sanda yadda ya ga dama har da kiran su barayi.

Hassan ya yi wa ‘yan sanda wankin babban bargo

A takardar rahoton farko da Sifeta Danjuma Hamidu ya gabatar gaban kotu, Bala ya ce ya gwammaci ya mutu akan ya shiga harkan ta’addanci irin ta ‘yan sanda.

Bayan ya amsa cewa ya kira. ‘yan sanda da barayi, a ranar Talata, 21 ga watan Satumba alkalin kotun, Hon Nuhu Musa Garta ya yanke masa shekaru 2 a gidan yari ko kuma ya biya tarar N50,000 kamar yadda LIB ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel