Ambaliyar ruwa a majalisa: Dan majalisa ya koka, ya ce akwai babbar matsala

Ambaliyar ruwa a majalisa: Dan majalisa ya koka, ya ce akwai babbar matsala

  • Dan majalisa ya koka kan yadda majalisar dattawa ke yawan samun ambaliyar ruwan sama
  • Ya bayyana kokawarsa ne yayin zaman majalisa a yau Laraba 22 ga watan Satumban 2021
  • Kakakin majalisa ya amince da a ba da umarnin gyara duba da muhimmancin zauren majalisar

Abuja - Ndudi Elumelu, shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, ya nuna damuwa kan yoyon rufin ginin majalisar dokokin kasar, TheCable ta ruwaito.

Elumelu ya yi magana a zauren majalisar yayin zaman majalisar wakilai na ranar Laraba 22 ga watan Satumba.

A cikin makwannin baya-bayan nan, ambaliyar ruwa ta mamaye zauren majalisar dokokin - yawanci bayan ruwan sama mai karfi. Ruwa ya sake mamaye ta bayan ambaliya a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF

Ambaliyar ruwa a majalisa: Dan majalisa ya koka, ya ce akwai babbar matsala
Yayin da ake kwashe ruwa daga majalisa | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Tushen ambaliyar an ce shine saman ginin majalisar, wanda ke da babban zauren da ke kaiwa zuwa zaurukan majalisar dattijai da na wakilai.

A zaman majalisar na ranar Laraba, Elumelu ya kawo shawarin daukar matakin gaggawa kuma ya ce mahaukaciyar ambaliyar tana da "hadari" ga 'yan majalisar.

Punch ta ruwaito Elumelu na cewa:

"Idan ba a yi wani abu don magance shi ba, babu wanda ran wani ke hannunsa, amma ba za mu iya fadin abin da zai iya faruwa ba."
“Da shigowa wannan wurin, zaku ga masu shara; suna ta tattara [debe] ruwan da ke saukowa daga wannan dakin.
"Kuma a gani na, yana da hadari mu ci gaba da kasancewa kan ayyukanmu na yau da kullum -wakiltar mutanenmu, yin magana a madadin mutanenmu, don samar da kyakkyawan doka.

Kara karanta wannan

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

“Don haka, ina kira ga mai girma kakakin majalisa, akwai bukatar a yi wani abu don magance wadannan magudanar ruwa da muke gani a cikin wannan zauren. Wannan shine magana ta. ”

Martanin kakakin majalisa

Da yake mayar da martani, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar, ya ce:

“Muhimmin lamari na gata wanda ya shafi zauren baki daya dangane da abubuwan more rayuwa a nan. An amince umarnin doka.”

A shekarar 2019, majalisar kasa ta yi kasafin sama da naira biliyan 30 don gyaran katafaren ginin.

Sai dai wasu 'yan Najeriya sun soki adadin kudin da aka ware don gyaran, sannan daga baya aka sake duba kasafin kudin zuwa naira biliyan tara.

A halin yanzu, babu wani aikin gyara kwanan nan da aka gudanar akan ginin.

Gwmnatin Buhari ta shirya kwato £200m da aka sace aka boye a Amurka

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kwato fam miliyan 200 da aka sace aka boye a Amurka, yayin da gwamnatin ke shirin fara kwato kadarori mallakin kasar.

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle ya sanar da dalilin da yasa suka daina sasanci da 'yan bindiga

Yunkurin ya fito ne ta bakin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami wanda ke magana a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a New York ta kasar Amurka.

Channels Tv ta tattaro cewa, da yake magana kan yaki da cin hanci da rashawa da kwararar kudade a kasar, Malami ya ce:

"Muna duba yiwuwar dawo da fam miliyan 200 da wasu kari amma to, hakan ba yana nufin babu wasu kadarorin da ake alaka da su ba, dangane da sauran kasashen duniya da suka hada da Ireland.

Asali: Legit.ng

Online view pixel