Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF

Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF

  • Dan majalisar dattawa daga jihar Oyo, Shina Peller, ya yi martani ga dattawan arewa kan matsayarsu a mika mulki ga kudu
  • Shina ya ce ba za ta yuwu ba a ce yankin arewacin Najeriya ne za su cigaba da mulkar kasar nan har abada, babu adalci a lamarin
  • Dan majalisar ya kara da cewa, hatta addinai suna son zaman lafiya, idan kuwa hakan ne, adalci ne kadai da daidaito zai tabbatar da shi

Oyo - Dan majalisa mai wakiltar mazabar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa a tarayya daga jihar Oyo a majalisar dattawa, Shina Peller, ya mayar wa dattawan arewa martani kan matsayarsu a mulkin karba karba a kasar nan.

A ranar Lahadin da ta gabata, Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar dattawan arewa, ya ce arewa ba za ta zuba ido ta zama ta biyu ba a 2023, ya kara da cewa yankin ne zai samar da shugaban kasan Najeriya na gaba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ku daina tsinewa shugabanninku saboda wahalar rayuwa – Sanusi ga ‘yan Najeriya

Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF
Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Amma kuma a wata takardar ranar Talata, Shina ya musanta cewa yawan kuri'un ba su ne ke nufin cewa za a yi burus da daidaito da adalci ba, Daily Trust ta ruwaito hakan.

"Ta yaya kungiyar dattawan arewa za ta sanar da 'yan Najeriya cewa ba zai yuwu a mika mulki hannun kudancin ba a 2023? Ban amince da matsayarku ba. Samun yawan kuri'u ba yana nufin za a yi biris da adalci tare da daidaito ba."
“Ko a matsayinmu na Musulmi, addininmu ya bukaci a zauna lafiya kuma in har ana so ya dawwama, dole ne a samu adalci da daidaito. Ba zai yuwu kuwa mulki ya dawwama a arewa ba.
“Muna sa ran kudu da arewa za su yi aiki tare wurin gina masana'antu masu karfi wurin tabbatar da hadin kai tare da kawo mulki kudanci a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Kaduna: Hotunan 'yan sanda masu murabus suna yi wa hukumar fansho zanga-zanga

“Wannan dama ce da za mu gyara matsalar da muka tarar tun kaka da kakanni ta yadda ba za mu rabe ba," yace.

Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna

A wani labari na daban, Andy Ubah, dan siyasan Najeriya da kasar Amurka da Ingila ke tuhumarsa kan sumogal din daloli na dab da zama gwamnan jihar Anambra.

Kasar Amurka ta binciki Uba kan wani al'amari da ta alakanta da damfara kamar yadda gwamnatin Amurka ta sanar, Premium Times ta wallafa hakan.

A Ingila inda aka haramta masa shiga, hukumomi sun ce dan siyasan Najeriya na da alaka da damfara da wasu al'amuran zargi kuma Ingila ba ta da bukatar ganin shi a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel