Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu karbuwa a jam'iyyun siyasa 17 na kudanci
- Wasu kungiyoyin siyasa a jihar Delta sun amince da tsayawar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa
- Wasu jam'iyyu 17 ne suka bayyana goyon bayansu ga tsayawar Atiku Abubakar a zaben 2023 mai zuwa
- Sun ce, Atiku ne ya fi cancanta ya tsaya takara a jam'iyyar PDP duba ga wasu halaye na kirki da yake dasu
Delta - Shugabannin jam’iyyun siyasa 17 da kungiyoyin farar hula a jihar Delta a ranar Lahadin da ta gabata sun amince da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.
Amincewar tana zuwa ne bayan bukatar gwamnoni jihohi 17 na kudancin kasar na neman shugaban kasa daga kudanci, Punch ta ruwaito.
Gamayyar kungiyar Atiku Support Groups Initiative wacce ta sanar da amincewar ta yi ikirarin cewa bai kamata kabilanci ko bambancin siyasa su zama abin duba ga tsayar da dan takarar shugaban kasa a 2023 ba.
Babban Darakta na ‘CASGI ATIKU 2023, Mista Obinna Okorie, ya fadi haka a lokacin kaddamar da kungiyar a garin Asaba.
Okorie ya ce:
“Najeriya ta yau ta sha fama da matsanancin rashin tsaro, rashin aikin yi, kange matasa da kuma yawan karbar bashi ba tare da samar da wani abin kirki ba, wanda hakan ya jefa babbar kasar mu cikin hadari.
"CASGI ATIKU 2023 PROJECT kungiya ce ta Najeriya da ta ratsa kabila, kungiyoyin siyasa da sauran abubuwan da ke karkashin kasa.
“Jam’iyyar PDP za ta bai wa Mai girma Atiku Abubakar tikitin takarar shugaban kasa a shekarar 2023 saboda, Atiku Abubakar shi ne wanda ya fi dacewa ya ja ragamar mulkin PDP kan karagar mulki idan aka yi la’akari da ayyukansa na baya da kuma nuna karfin arzikinsa da gina tattalin arziki.”
Shugaban kasa a 2023: Kudu ba za ta goyi bayan duk jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa ba, in ji gwamnan APC
Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana abin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan Tinubu
A gefe guda, wani dan jam'iyyar APC mai mulki, Musa Sarkin Adar, ya bayyana dalilin da ya sa jam'iyyar mai mulki ke zawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Adar babban dan majalisar wakilai ne daga Sakkwato kuma shugaban kwamitin majalisar akan man fetur.
Legit.ng ta tattaro cewa yayin da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Arise, ya ce kakakinsa ya karyata jita -jitar da ake yadawa game da komawar Jonathan APC.
Sai dai kuma, ya bayyana cewa abin da ke ƙasa shine cewa jam’iyya tana da 'yanci kuma tana iya jan hankalin duk wanda take tunanin zai ƙara ƙima a gare ta.
Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP
A wani labarin daban, Daily Trust ta tabbatar da ficewar Sani daga hannun hadiminsa na kusa, Malam Suleiman Ahmed a makon jiya.
Ahmed ya ce mai gidan nasa ya sauya sheka ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, lokacin da yake ganawa da wasu jiga-jigan PDP a Kaduna.
Shin me Sanata Sani zai samu da shiga jam'iyyar adawa ta PDP?
A shekarar 2015, an zabi sanata Shehu Sani don wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki. Ya kasance mai sukar lamirin da kalubalantar lamurra da dama.
Asali: Legit.ng