Rikici ya barke tsakanin matasa, an harbe fasto yayin da yake tsaka da ibada

Rikici ya barke tsakanin matasa, an harbe fasto yayin da yake tsaka da ibada

  • Rikici ya barke tsakanin matasa, an harbe fasto yayin da yake ibadar sanyin safiya a Abakaliki
  • Rahotanni sun bayyana cewa, wasu matasa ne suka tada rikici bayan samun labarin an kashe dan uwansu
  • 'Yan sanda sun kawo dauki, lamarin da ya kai harbe-harbe har aka samu faston da bai ji ba bai gani ba

Ebonyi - An kashe wani fasto, John Onu na cocin Glorious Gospel Fire Assembly dake Abakaliki da wani saurayi da har yanzu ba a bayyana sunansa ba a jihar Ebonyi sakamakon tashin hankali tsakanin matasa da ya barke a daren Lahadi har zuwa safiyar Litinin.

An ce harsashe ne ya kurkure ya samu faston yayin da yake addu’a a gidansa da ke Hatchery, titin Nkaliki na Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi lokacin da jami’an tsaro suka kai samame a wani otel da ke yankin da matasa ke rikici.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

Rikici ya barke tsakanin matasa, an harbe fasto yayin da yake tsaka da ibada
Rikici ya rutsa da fasto | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Meye ya jawo tashin hankalin?

Leadership ta tattaro cewa fusatattun matasa na Ebyia Upnuhu, karamar hukumar Abakaliki na jihar da yawansu ya haura 50 sun tada rikici, tare da kona gidaje a yankin bayan da aka yi wa wani mutum a cikin al’umma dukan tsiya har ya mutu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban karamar hukumar Abakaliki, Mista Emmanuel Nwangele wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya bayyana abin a matsayin abin takaici kuma abin kyama.

Matasan wadanda suka fusata da samun labarin mutuwar mutumin sun bar garin suka zo Abakaliki, da safiyar Litinin inda suka lalata wani otel na wani mutum Chukwudi Onyibe.

An ta tattaro cewa Mista Onyibe shine mataimaki na musamman ga shugaban karamar hukumar, Hon Emmanuel Nwangele kan kudaden shiga na cikin gida, haka Daily Sun ta rahoto.

An kuma ruwaito cewa an tura ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru, wanda ya kai ga harbe-harbe don tarwatsa matasan tare da hana su kona otal din.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An bindige dan fashin daji a babban titin Kaduna zuwa Abuja

An tattaro cewa harsashi ya kuskure ya samu Fasto John Onu wanda ke zaune a gaban otal yayin da yake gudanar da ibadar safiya. Rahotanni sun ce harsashin ya same shi a gefen zuciyarsa sannan ya huda bayansa.

Har ila yau matasan sun yi yunkurin kai hari hedikwatar karamar hukumar Abakaliki, Nakaliki amma jami'an tsaro sun tarwatsa su.

Yan kudu: Son kai ne Buhari ya yi sansanin sojin ruwa a Kano bai yi a Bayelsa ba

A wani labarin, Dattijo kuma babban jigon kabilar Ijaw, Cif Edwin Clark, ya caccaki Babban Hafsan Sojojin Ruwa (CNS), Admiral Awwal Zubairu, kan shirin rundunar sojin ruwan Najeriya na kafa sansanin sojan ruwa a jihar Kano.

A wata budaddiyar wasika da ya aike ga CNS a ranar Litinin, 20 ga Satumba, Clark ya yi tir da amincewa da kafa sansanin sojojin ruwa a Kano, yana mai cewa matakin yana daya daga cikin ayyukan son kai da gwamnatin Buhari ke jagoranta.

Kara karanta wannan

APC ta kare Buhari, ta fadi dalilan gwamnatin tarayya na karbo bashin tiriliyoyi bini-bini

Wani yanki daga cikin wasikar da jaridar The Punch ta wallafa ya ce:

"Cewa ana gina sabon sansanin sojan ruwa a tsakiyar sahel wanda duk duniya ta sani a halin yanzu na fuskantar barazanar hamada da ke yaduwa cikin sauri kuma ba tare da wani la'akari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel