Da duminsa: An bindige dan fashin daji a babban titin Kaduna zuwa Abuja

Da duminsa: An bindige dan fashin daji a babban titin Kaduna zuwa Abuja

  • Jami'an tsaro sun harbe wani gagarumin dan fashin daji a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja
  • An gano cewa an harbe shi ne a sa'o'in farko na ranar Alhamis yayin da suka yi artabu da jami'an tsaro
  • Lamarin ya auku ne wurin kauyen Kasarami kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar

Kaduna - Wani gagrumin dan fashin daji da ke daga cikin kungiyar da ta kware wurin addabar jama'ar jihar Kaduna, ya sheka lahira bayan an bindige shi.

Daily Trust ta tattaro cewa, an halaka dan bindigan ne yayin da yayi kokarin musayar wuta da jami'an tsaro da ke wuraren kauyen Kasarami da ke babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Da duminsa: An bindige dan fashin daji a babban titin Kaduna zuwa Abuja
Da duminsa: An bindige dan fashin daji a babban titin Kaduna zuwa Abuja
Asali: Original

Lamarin ya auku ne a sa'o'in farko na ranar Alhamis kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe

Wani shugaban matasa wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce an sheke farar hula biyu yayin da aka ragargaza motar jami'an tsaro yayin musayar wuta da miyagun.

Lamarin ya auku ne kasa da sa'o'i 48 bayan miyagu sun sace Sarkin Bungudu na jihar Zamfara a kan babbar hanyar.

Shugaban matasan ya ce:

"An kashe wani dan bindiga yayin da aka yi musayar ruwan wuta da jami'an tsaro."
"Wani direba da kwandastansa wadanda ke hanyar wucewarsu yayin da lamarin ke faruwa sun sheka barzahu."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

‎Ya ce jami'an tsaro sun bankado harin kuma an sheke dan bindiga daya yayin da matafiya biyu suka bakunci lahira.

Kaduna: Kotu ta bukaci malami da ya katse soyayyar da ke tsakaninsa da dalibarsa

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Wani jirgin yaki ya yi luguden wuta a Yobe ya kashe fararen hula da dama

A wani labari na daban, wata kotun shari'a da ke zama a Magajin Gari, Kaduna, a ranar Laraba ta umarci wani malamin makaranta, Yusuf Yusuf da ya datse dukkan wata soyayya da ke tsakaninsa da dalibarsa mai suna Zainab Muhammad.

Alkali Murtala Nasir, ya umarci malamin da ya biya N8, 500 ga Zainab a matsayin kudin shigar da kara da kuma kudin asibiti da ta biya bayan mugun dukan da yayi mata.

Alkalin ya yanke wannan hukuncin bayan sasancin da su biyun suka yi ba a kotu ba, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng