Abun Kunya: Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa Yar Shekara 19 Ciki, Yan Sanda Sun Damke Shi

Abun Kunya: Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa Yar Shekara 19 Ciki, Yan Sanda Sun Damke Shi

  • Rundunar yan sanda reshen jihar Ogun, ta bayyana cewa ta damke wani mutumi da ya yi wa yarsa da ya haifa ciki
  • Kakakin yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, yace ɗiyar mutumin ce ta kawo rahoton abinda mahaifinta ya jima yana mata
  • Kwamishinan yan sandan Ogun ya bada umarnin maida lamarin sashin binciken manyan laifuka domin ɗaukar mataki na gaba

Ogun - Rundunar yan sanda reshen jihar Ogun ta cafke wani mutumi ɗan kimanin shekara 45, Olaoluwa Jimoh, da zargin ɗirkawa ɗiyarsa ciki a yankin Ode-Remo, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin rundunar yan sandan Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya fitar.

Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa Yar Shekara 19 Ciki
Abun Kunya: Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa Yar Shekara 19 Ciki, Yan Sanda Sun Damke Shi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani sashin jawabin yace:

"Hukumar yan sanda ta damƙe Jimoh a ranar 16 ga watan Satumba bisa zargin ɗirkawa yarsa da ya haifa ciki, yar kimanin shekara 19."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Aure Mai Shayarwa da Wani Ɗan Kasuwa a Jalingo

"An cafke mahaifin ne biyo bayan ƙarar da ɗiyarsa ta shigar a ofishin yan sanda dake yankin Ode-Remo."
"Budurwar ta shaidawa yan sanda cewa mahaifinta ya yi lalata da ita a lokuta da dama, kuma ya mata barazanar kisa matukar ta tona masa asiri."

Ina mahaifiyarta take?

DSP Oyeyemi ya ƙara da cewa ɗiyar ta faɗawa yan sanda cewa mahaifinta da mahaifiyarta sun rabu shekaru da dama da suka shuɗe, Punch ta ruwaito.

"Tana zaune tare da mahaifiyarta kafin shekaru biyu da suka wuce, lokacin da mahaifin ya bukaci tazo ta zauna tare da shi."
"Bayan samun rahoton, DPO na yankin ya umarci jami'ansa su yi gaggawar kamo mutumin, kuma suka samu nasarar damke shi."

Mutumin ya amsa laifinsa

Yayin gudanar da bincike, mutumin da ake zargin ya amsa laifinsa amma ya bayyana cewa sheɗan ne ya rinjaye shi.

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Mutum 6 Sun Mutu Yayin da Miyagun Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari Sokoto

A halin yanzun kwamishinan yan sandan jihar, CP Edward Ajogun, ya bada umarnin maida lamarin sashin binciken manyan laifuka domin tsananta bincike da kuma gurfanar da mai laifin.

A wani labarin kuma rundunar soji ta bayyana irin tasirin da addu'o'in yan Najeriya ƙe yi a yaƙi da Boko Haram

Kwamandan rundunar Operation Haɗin Kai, Christopher Musa, yace addu'ar yan Najeriya ce take sa mayakan Boko Haram miƙa wuya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Musa yace sojoji sun samu gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da yan ta'addan Boko Haram da kuma ISWAP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262