Barin wuta ta sama: Gwamnan Yobe ya umurci asibitocin gwamnati da su kula da wadanda suka jikkata
- Gwamnatin jihar Yobe ta umarci asibitocin gwamnati da ke Geidam da Damaturu da su kula da wadanda suka jikkata a farmakin jirgin yaki a ƙauyen Buhari da ke ƙaramar hukumar Yunusari
- Gwamna Mai Mala Buni ne ya bayar da wannan umurnin a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba
- Buni ya kuma yi umarnin gudanar da bincike don gano musabbabin barin wutan
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala-Buni, ya umarci asibitocin gwamnati da ke Geidam da Damaturu da su bayar da magunguna kyauta ga waɗanda suka samu raunuka a lokacin farmakin jirgin yaki a ƙauyen Buhari da ke ƙaramar hukumar Yunusari ta jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yada labarai na jihar, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba.
Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi
Mala-Buni ya kuma umarci Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar da ta samar da kayan agaji don biyan bukatun gaggawa na iyalan mamatan da sauran mutanen gari, jaridar Punch ta ruwaito.
Ya umarci mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tsaro, Janar Dahiru Abdulsalan, mai ritaya, da ya yi hulda da rundunar sojojin sama ta Najeriya da rundunar hadin gwiwa don gano musabbabin barin wutan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
“Gwamnati za ta yi aiki kafada da kafada da jami’an tsaro, musamman rundunar sojojin saman Najeriya, don tabbatar da abin da ya faru a zahiri. Wannan yana da matukar mahimmanci kuma ya zama dole a gare mu don kiyaye faruwan haka a nan gaba da kuma kare rayukan mutanen mu.”
Buni ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar na hada kai da dukkan hukumomin tsaro don tabbatar da tsaron lafiyar mutane, jaridar Sun ta kuma ruwaito.
Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan al’umman gari? Rundunar soji ta yi martani kan rahoton
A baya Legit.ng ta kawo cewa an yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa wani jirgin sama mallakar rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya kashe mazauna wani gari a jihar Yobe.
Legit.ng ta tattaro cewa mai magana da yawun NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya yi wannan karin haske a cikin wani rubutu da aka yada a shafin Facebook na Aso Rock Villa a ranar Laraba, 15 ga Satumba.
Ions Intelligence, wata kungiyar tsaro ta yi zargin cewa jiragen yakin NAF yayin da suke aikin yaki da Boko Haram da ISWAP sun jefa bana-bamai bisa kuskure a Kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari wanda ya kashe mazauna yankin da dama tare da jikkata wasu.
Asali: Legit.ng