Addu'o'in Yan Najeriya Sun Fara Kama Mayaƙan Boko Haram, Rundunar Sojoji
- Rundunar sojoji ta bayyana cewa mika wuyan mayakan Boko Haram ya na da alaƙa da addu'o'in yan Najeriya
- Kwamandan Operation Hadin Kai, Christopher Musa, yace lamarin miƙa wuyan daga Allah ne, shine yake canza musu tunani
- Musa yace sojoji sun samu gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da yan ta'addan Boko Haram da kuma ISWAP
Borno - Kwamandan rundunar Operation Haɗin Kai, Christopher Musa, yace addu'ar yan Najeriya ce take sa mayakan Boko Haram miƙa wuya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Musa ya faɗi haka ne yayin da yake fira da manema labarai a kan halin da ake ciki game da yaki da yan ta'adda a arewacin Najeriya.
Kwamandan yace rundunar ta samu gagagrumar nasara kan mayaƙan Boko Haram da kuma abokiyar hamayyarta ISWAP.
Shin meyasa yan ta'adda suke tururuwan miƙa wuya?
Dangane da yan ta'addan dake mika wuya ga rundunar soji, Musa ya alaƙanta wannan nasarar da yawan addu'o'in yan Najeriya, yace, "Abun ya yi kama da Allah ya shiga lamarin."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Musa yace:
"Wasu daga cikin waɗanda suka miƙa wuya sun bayyana cewa basu san ya akai suka mika wuya ba kuma suna cigaba da aje makamai."
"Yana daga cikin horon da aka ba mu da kuma dokokin mu cewa idan kana yakar mutum, sai ya mika wuya gareka to ba zaka harbe shi ba, sannan idan ka kama shi zaka ji kansa kamar kowane mutum"
""Amma wasu suna kallon muna shagwaɓa su ne kuma sam ba haka bane, muna yin abinda ya dace ne, kuma tabbas doka zata yi aikinta"
Muna bukatar haɗin kan kafafen watsa labarai
Kwamandan ya yi kira ga kafafen watsa labarai su cigaba da nuna goyon bayansu ga namijin kokarin jami'an sojoji.
Ya ƙara da cewa rundunar soji zata cigaba da baiwa kafafen dukkan bayanan da ya kamata game da Operation ɗin da take gudanarwa.
A wani labarin kuma Sheikh Zazkazky Ya Gana da Mutanen da Suka Tsira da Rayuwarsu a Rikicin Mabiya Shi'a da Sojoji a 2015
Hakanan kuma Shehin malamin ya gana da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a rikicin.
Dailytrust ta rahoto cewa Zakzaky ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa iyalan ta'aziyya bisa rasuwar yan uwansu.
Asali: Legit.ng