Sanata Ndume: Kisar Kiyashin Da Sojoji Ke Yi Wa 'Yan Bindiga Ya Yi Dai-Dai
- Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya ce yana goyon bayan ragargazan da sojoji ke yi wa 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma
- Sanatan ya ce 'yan bindigan sun dade suna adabar mutane don haka bai ga laifi ba don a bi da su ta hanyar da suka zaba tunda ba su son zaman lafiya
- Ndume ya yi kira ga 'yan jarida su rika yin adalci wurin rahoton batutuwa da suka shafi tsaro da yaki da ta'addanci
Abuja - Shugaban kwamitin kan sojoji na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya goyi bayan ragargazar da sojoji ke yi wa 'yan bindiga, har da masu garkuwa da mutane a yankin arewa maso yammacin kasar, The Guardian ta ruwaito.
A cewar rahoton na The Guardian, Ndume ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa sun yanke shawarar cewa sojojin su fada wa 'yan bindigan da yaki ne bisa dokar aikin soja na kasa da kasa.
Sanatan na jihar Borno ya ce rahoton cewa ana take hakkin bil-adama na 'yan bindigan ba dai-dai bane duba da irin azaba da suka jefa al'umma ciki a baya-bayan nan.
Ya ce:
"Bayan jin wannan irin abin. Ina rokon ku, 'yan jarida, ku rika adalci wurin wallafa rahotannin ku. Muna fama da babban matsala ta 'yan bindiga da masu garkuwa, kuma ya shafe mu duka.
"Idan sojoji sun yi hubbasa sun fara kai wa 'yan bindigan hari suna samun nasara, abin da za ka fara ji shine take hakkin bil-adama da sauransu.
"Toh, ina batun hakkin mutanen da 'yan bindigan ke kashe wa, matar da aka cin zarfinsu ko kuma sojojin mu da ake yi wa kwantar bauna a kashe?"
Gwamna Buni ya jajantawa mutanen kauyen Buhari
Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya jajantawa iyalan mutane 30 da harin jiragen yaki na NAF da yi wa barna a kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari.
A ranar Laraba, jirgin yakin NAF, cikin kuskure ya harbawa mazauna kauyen bam yayin da ya ke sintiri kan iyakar Nigeria da Jamhuriyar Nijar.
'Yan bindiga sun afka gidan gona, sun sace wani babban ɗan kasuwa, sun bindige wani mutum
A wani labari daban, 'yan bindiga sun sace wani mai gidan gona, Jide Lawal, a gidan gonarsa da ke unguwar Agohun, Emoren - Imota, wani gari da ke kan iyakar jihar Legas da Ogun, The Punch ta ruwaito.
Punch Metro ta ruwaito cewa Lawal ya ziyarci gidan gonarsa ne a ranar Laraba don duba yadda abubuwa ke tafiya, amma sai wasu mutane da bindiga suka tare shi a kofar shiga.
An ce dan kasuwan na jira mai gadi ya bude masa kofa ne a lokacin da maharan suka yi amfani da damar suka tare shi.
Asali: Legit.ng