Sheikh Zazkazky Ya Gana da Mutanen da Suka Tsira da Rayuwarsu a Rikicin Mabiya Shi'a da Sojoji a 2015
- Sheikh Ibrahim Zakzaky ya gayyaci ɗaukacin mabiyansa da suka tsira daga rikicin da ya faru da sojoji a Disamba 2015
- Malamin yayi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa yan uwansu tare da ba su hakurin rashin zuwa har gida yin ta'aziyya
- Mutanen sun nuna jin daɗinsu bisa halin dattako da jagoransu ya nuna musu duk da halin da yake ciki
Zaria - Shugaban ƙungiyar mabiya shi'a (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya gana da mabiyansa da suka tsira da rayuwarsu a rikicin da ya faru tsakaninsu da sojoji a watan Disamba 2015.
Hakanan kuma Shehin malamin ya gana da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a rikicin.
Dailytrust ta rahoto cewa Zakzaky ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa iyalan ta'aziyya bisa rasuwar yan uwansu.
Malamin ya roke su da su tuna da irin matsanancin halin da jikan Manzon Allah (SAW), Imam Husaini, ya shiga a lokacin da aka kashe shi.
Bugu da kari jagoran mabiya mazhabar shi'a ya yi wa waɗanda suka samu halartar ganawar Nasiha da cewa kowace irin sadaukarwa ƙarama ce matukar kana kan gaskiya.
El-Zakzaky ya basu hakuri
Sheikh Zakzaky ya baiwa mutanen hakuri bisa gayyatarsu da ya yi, maimakon ya ziyarce su har gida domin jajanta musu.
Malamin yace:
"Saboda raunukan da na samu yayin harin sojojin, har yanzun muna ɗauke da harsasai a cikin jikin mu."
"Ba zamu iya zuwa gidajen kowanne daga cikin waɗanda lamarin Disamba 2015 ya shafa ba."
Daganan sai malamin ya yi addu'ar Allah ya baiwa iyalan waɗanda suka rasa yan uwansu kwarin guiwar jure rashin da suka yi.
Mutanen sun yaba jagoransu
Dr. Isa Waziri Gwantu, wanda ya bayyana cewa ya rasa ƴaƴansa huɗu a lamarin, ya nuna jin daɗinsa bisa gayyatar da Malamin ya musu duk da matsanancin halin da ake ciki.
Gwantu ya ƙara jandada cewa wannan abun da ya faru ba zai sanya su ja da baya daga hanyar gaskiya da Zakzaky ke jagorantarsu ba.
Hajiya Jummai Karofi, wadda tace ta rasa ƴaƴanta biyar a rikicin, tace: "Inason waɗanda suka kashe ƴaƴa na su sani cewa abinda suka yi ba zai bamu tsoro mu bar tafiyar Sheikh Zakzaky ba."
A wani labarin kuma Kakakin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya mika takardar murabus daga kan mukaminsa ga shugabannin jam'iyyar
A cikin takardar mai ɗauke da kwanan watan 19 ga watan Satumba, Chief Ogbonna Nwuke, yace lokaci ya yi da zai fuskanci wasu abubuwan na daban.
Tsohon kakakin ya mika godiyarsa ga kowa da kowa na cikin jam'iyyar APC musamman mambobi waɗanda suka ba shi goyon baya.
Asali: Legit.ng