Da Dumi-Dumi: Kakakin Jam'iyyar APC Mai Mulki Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Da Dumi-Dumi: Kakakin Jam'iyyar APC Mai Mulki Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

  • Kakakin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya mika takardar murabus daga kan mukaminsa ga shugabannin jam'iyyar
  • A cikin takardar mai ɗauke da kwanan watan 19 ga watan Satumba, Chief Ogbonna Nwuke, yace lokaci ya yi da zai fuskanci wasu abubuwan na daban
  • Tsohon kakakin ya mika godiyarsa ga kowa da kowa na cikin jam'iyyar APC musamman mambobi waɗanda suka ba shi goyon baya

Rivers - Kakakin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan reshen jihar Ribas, Chief Ogbonna Nwuke, ya yi murabus daga kan mukaminsa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Nwuke, ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa shugabannin jam'iyyar mai ɗauke da kwanan watan 19 ga watan Satumba.

Kakakin APC na ribas ya bayyana cewa ya ɗauki matakin sauka daga mukaminsa ne a karan kansa.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa mambobin APC ke jin haushin shigowar Kayode jam'iyyarsu, DG PGF

Kakakin APC ya yi murabus
Da Dumi-Dumi: Kakakin Jam'iyyar APC Mai Mulki Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Meyasa ya yi murabus?

Punch ta rahoto a wasikar da Nwuke ya aike wa shugabannin jam'iyya, yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna da tabbacin cewa aikin da aka bamu, mun kammala shi, mun zo wannan matakin (Kakakin APC) dai-dai lokacin da yake da ƙalubale sosai."
"Duk abinda yake da farko to yana da ƙarshe, lokaci ya yi da zamu matsa mu baiwa wasu wuri, kuma lokaci ne da ya dace mu maida hankali kan wasu abubuwan na rayuwa."

Nwuke ya gode wa kowa a APC

Tsohon kakakin APC ya godewa abokan aikinsa a jam'iyyar APC musamman mambobin jam'iyya bisa kwarin guiwar da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa.

"Mun amfana matuka da irin goyon bayan da mambobi suke ba mu, da kuma kwarin guiwa da fatan alkairin da suka kasance suna mana."
"Yayin da muke jiran ta Allah ta kasance da kuma tsarin da Ubangiji ya mana a rayuwa, mun yi iyakar bakin ƙoƙarin mu wajen sauke nauyin da aka ɗora mana."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP

A wani labarin kuma Ministan Buhari ya roki likitoci su taimaka su janye yajin aikin da suke yi har tsawon watanni

Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya yi kira ga likitoci masu neman kwarewa su taimaka su janye yajin aki.

Ministan yace yana da ƴaƴa da suke cikin ƙungiyar NARD, babu dalilin da zai ci mutuncin likitocin, sai dai ya kare su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262