Ku Taimaka Ku Koma Bakin Aiki, Ministan Buhari Ya Roki Likitoci

Ku Taimaka Ku Koma Bakin Aiki, Ministan Buhari Ya Roki Likitoci

  • Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya yi kira ga likitoci masu neman kwarewa su taimaka su janye yajin aki
  • Ministan yace yana da ƴaƴa da suke cikin ƙungiyar NARD, babu dalilin da zai ci mutuncin likitocin, sai dai ya kare su
  • A cewarsa Kotu ta yanke hukuncin cewa likitocin su koma bakin aiki, sannan su dawo a cigaba da zama teburin sulhu

Abuja - Ministan kwadugo, Dakta Chris Ngige, ya roki kungiyar likitoci masu neman kwarewa da su janye yajin aikin da suke yi yayin da za'a cigaba da tattaunawa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ngige ya yi wannan rokon ne yayin fira da kafar watsa labarai ta Channels TV a shirin su na 'Sunday Politics,' dai-dai lokacin da yajin aikin likitocin ya shiga rana ta 59.

Ministan kwadugo, Chris Ngige
Ku Taimaka Ku Koma Bakin Aiki, Ministan Buhari Ya Roki Likitoci Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ministan yace:

"Ina kira ga ƙungiyar NARD ta sake nazari kan matakin da ta ɗauka, ku koma bakin aiki gobe ko jibi, sannan ku dawo mu cigaba da zama teburin sulhu. Akwai abubuwa da dama da ya kamata mu tattauna."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Inada ƴaƴan yan uwana waɗanda likitoci ne masu neman ƙwarewa, akwai mutum uku a asibitin koyarwa na Nnamdi Azikwe, UNTH Enugu, suna da yawa."
"Ɗan dana haifa zai kammala ƙaratun likitanci a watan Oktoba mai zuwa, babu yadda za'ayi in wulakanta likita, sai dai in kare shi."

Wane hukunci kotu ta yanke?

Ministan ya yi tsokaci kan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar gaban kotu kan yajin aikin da likitocin suka shiga.

"Kotu ta yanke hukunci, kuma tace 'Ku je ku sasanta tsakanin ku amma a halin yanzun ku koma bakin aiki sai a cigaba da zaman tattaunawa."

Su wa suka shigar da ƙarar?

Ngige yace ma'aikatar lafiya da kuma ofishin Antoni Janar na ƙasa, su ke da alhakin janye ƙarar da gwamnati ta shigar a gaban kotu.

A wani labarin kuma Mutum 6 Sun Mutu Yayin da Miyagun Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari Sokoto

Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari ƙauyen ƙaramar hukumar Tangaza, inda suka hallaka mutum shida.

Rahotanni sun tabbatar da cewa miyagun maharan sun harbe mata biyu har Lahrira, sannan suka yanka wasu matasa huɗu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel