Jigon APC a Kano ya yi tir da tarbar da Buhari, APC suka yi wa Fani-Kayode a fadar Aso Villa

Jigon APC a Kano ya yi tir da tarbar da Buhari, APC suka yi wa Fani-Kayode a fadar Aso Villa

  • Tarbar da aka yi wa Femi Fani-Kayode a jam’iyyar APC ya bata wa wasu rai
  • Muaz Magaji ya caccaki yadda aka karbi tsohon rikakken ‘dan adawar a APC
  • ‘Dan siyasar ya yi magana a Facebook, ya gaza gane hikimar abin da ya faru

Kano - Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Muaz Magaji ya tofa albarkacin bakinsa a game da sauya-shekar Femi Fani-Kayode zuwa APC.

Muaz Magaji wanda aka fi sani da ‘Dan sarauniya ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda shugabannin APC suka karbi tsohon Minista, Femi Fani-Kayode.

Injiniya Magaji ya fito shafinsa na Facebook, yana sukar fadar shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Mala Buni.

Haka zalika jagoran na jam’iyyar APC a Kano ya yi Allah-wadai da wasu malamai. Ana zargin Magaji yana shagube ne ga Ministan sadarwa, Isa Ibrahim Pantami.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Hakan na zuwa ne bayan Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya shirya liyafa ta musamman a gidansa a Abuja, ya tarbi tsohon ‘dan adawar da ya rika sukarsa a can baya.

Tsohon kwamishinan yake cewa sauya-shekar Fani-Kayode ta sa ya shiga tunanin makomar Arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fani-Kayode a fadar Aso Villa
Femi Fani-Kayode ya shiga jam’iyyar APC Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Menene Dansarauniya ya rubuta a Facebook?

Shugaban tafiyar ta Win-Win 2023, yace a irin wannan tafiya, ya gagara fahimtar makasudin kafa jam’iyyar APC da kifar da gwamnatin PDP da aka yi a zaben 2015.

“Dawowar [Femi] Fani Kayode (FFK) APC da irin karbar da akai masa a fadar Shugaban kasa, da gidajen malaman mu, da shugabanin siyasar mu...Ni kam tasa na fara tunani shin ko munsan me yankinmu da Alumarmu ke fuskanta kuwa a Jamhuriyar Nigeria?”
“Shin meye matsayin APC kan makoma da hantarar da ake yiwa Alumar mu a kasarnan? Shin me muka zo canzawa ne a 2015…”

Kara karanta wannan

Farfesan jami'ar Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce yayin sallar Juma'a

“Kuma su waye ne a ka gaya mana sun jefa mu a halin da muka shiga a baya na zulumi, talauci, da gallazawa talaka...?

Daga baya an ga Magaji ya rubuta: “PayMe Fani Kayode (FFK) Decamped to All (Sort of) People Congregation (APC)”

Haka zalika ya maimaita abin da wani ya fada a Facebook, yace:

“Yawancin masu sukata basu san abinda PayMe Fani Kayode ya fada akan Arewa, Hausa/Fulani, da Muslunci ba lokacin yana PDP.”

FFK zai yi takara a APC?

A ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba, 2021, aka ji labari cewa har fastocin takarar Femi Fani-Kayode da Gwamnan Kogi, Yahaya Bello a APC sun fara yawo

Amma shugaban kungiyar Magoya-bayan nan ta Nigeria youths Awareness Group for Yahaya Bello, 2023 yace babu hannunsu wajen fito da wadannan fastoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel