Ina gidan Farfesa Pantami jiya har cikin dare, mun debi girki kuma mun tattauna: Femi Fani-Kayode
- Ministan Sadarwa ya shirya liyafa ta musamman wa sabuwar amaryar APC, Femi Fani-Kayode
- Fani Kayode ya bayyana cewa ya ji dadin gayyatar da Farfesa Pantammi ya masa
- Yace suna gidan har cikin dare suna tattaunawa
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya yi takakkiya zuwa gidan Ministan Sadarwa da tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami dake birnin tarayya Abuja.
Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook, Fani-Kayode yace Farfesa Pantami ne ya gayyacesa kuma ya amsa.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi wa Femi Fani-Kayode rakiya yayin ziyarar.
Fani Kayode ya kara da cewa sai da suka kwashe awanni suna tattaunawa har cikin dare.
A cewarsa:
"Na samu matukar karamci tare da abokina, Gwamna Bello Matawalle, na Zamfara lokacin da aka gayyacemu kyakkyawar gidan abokina kuma dan'uwana Farfesa Isa Pantami, da daren jiya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Muna wajen har awannin farko na safiya, mun kwashe lokaci sosai kuma mun tattauna abubuwa da dama da kuma cigaba."
Yan Nigeria da dama na tofa albarkacin bakinsu kan wannan sabuwar 'abokantaka da zumunci' da ke ƙuluwa tsakanin Fani-Kayode da jiga-jigan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tun bayan komawarsa APC da ya daɗe yana suka.
Ga wasu daga cikin maganganun masu bibiyanmu:
Aminu Abdullahi yace:
"Wallahi duk Nigeria babu tsinanne la'ananne, makiyin musilmi da musilinci irin kayode, wai Amma yau shine kuke jawoshi Ajikinku, harda shiyamasa walima,
Andai ji kunya wallahi"
Abdullah Caleepha yace:
"wannan shine halin salihan bayi..yafewa wanda ya cuce ka ko yaci mutuncin ka a baya..sanadiyyar kyawawan halin ka... Allah xai sa ya shiryu ya kuma yi nadamar abin da yayi a baya.
Kuma ka sani cewa ba haka kawaii ya shirya musu liyafa ba.. zuwa sukayi akan yanda xa'a magance harkar tsaro shine dalilin
Allah yasa mu dace... ameen"
Danbaba Y Abdullahi LK yace:
Wani lokacin sai anbi hanyar 6arna 1 kafin asamu damar gyara 10! Allah yaci gaba da yiwa mal, prof isa ali fantami jagora.
Usman Abdullahi yace:
Duk cikin su nafi jin tausayin Pantamin. Kamar dai rudin duniya ta dauke shi ya manta shi wanene. Allah Ya Gafartawa Sheikh Albanin Zaria. Shi kam yaki ya karbi muƙamin Gomnati dan kare martabar ilminsa da mutuncinsa.
Asali: Legit.ng