Labari Da Duminsa: Mutum 6 Sun Mutu Yayin da Miyagun Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari Sokoto

Labari Da Duminsa: Mutum 6 Sun Mutu Yayin da Miyagun Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari Sokoto

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari ƙauyen ƙaramar hukumar Tangaza, inda suka hallaka mutum shida
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa miyagun maharan sun harbe mata biyu har Lahrira, sannan suka yanka wasu matasa huɗu
  • Wannan harin yazo awanni ƙaɗan bayan wasu fusatattun mutane sun hallaka tare da ƙone gawarwakin yan bindiga 13 a garin Tangaza

Sokoto - Yan bindiga sun kai sabon hari wani ƙauye a ƙaramar hukumar Tangaza, jihar Sokoto, inda suka hallaka mutum shida, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki ƙauyen, wanda mafi yawancin mutanen cikinsa mafarauta ne, da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Kuma yan bindigan sun kai harin ne dai-dai lokacin mafi yawan mazan garin sun fira sana'arsu ta farauta.

Kara karanta wannan

Makiyayi da shugaban Fulani sun sheka lahira bayan 'yan bindiga sun kai farmaki Kaduna

Yan bindiga sun kai sabon hari Sokoto
Labari Da Duminsa: Mutum 6 Sun Mutu Yayin da Miyagun Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari Sokoto Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Shin harin yana da alaƙa da kashe yan bindiga 13?

Sai dai babu tabbacin cewa ko harin miyagun yana da alaƙa da kashe yan bindiga 13 da mutane suka yi, waɗanda suka kai hari garin Tangaza ranar Asabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta shaidawa Dailytrust cewa wasu mata biyu na cikin waɗanda miyagun maharan suka hallaka a lokacin harin.

Yace:

"Sun bindige mata guda biyu har Lahira, yayin da suka yanka matasa guda huɗu yayin mummunan harin."
"Dukka yan bijilanti da kuma yan sa kai dake yankin sun bazama cikin daji domin neman waɗanda suka aikata wannan mummunan ta'addancin."

Mutane sun sheke yan bindiga 13

A ranar Asabar, fusatattun mutane suka sheƙe tare da ƙone gawarwakin wasu yan bindiga 13, waɗanda suka kai hari garin Tangaza suka kashe mutum huɗu.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana lokacin da gwamnatinsa zata ɗage hana amfani da hanyoyin sadarwa

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Kutsa Supermarket Suka Harbe Wani Lauya Har Lahira

Matawalle yace gwamnatinsa zata cigaba da tattaunawa da hukumomin tsaro lokaci bayan lokaci domin jin halin da ake ciki.

Gwamnatin Katsina ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumi 13 daga cikin 34 dake faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262