Labari Da Duminsa: Sanata Shehu Sani Ya Koma Jam'iyyar PDP

Labari Da Duminsa: Sanata Shehu Sani Ya Koma Jam'iyyar PDP

  • Mai rajin kare hakkin bil-adama, Sanata Shehu Sani ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP
  • Malam Suleiman Ahmed, hadiminsa ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis 16 ga watan Satumba
  • Ahmed ya ce Shehu Sani ya koma PDP ne a yau bayan ganawa da jiga-jigan jam'iyyar a Kaduna

Kaduna - Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta Tsakiya a Majalisa ta 8 daga 2015 zuwa 2019, ya shiga jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP), Daily Trust ta ruwaito.

Sani, wanda aka zabe shi a matsayin sanata a karkashin jam'iyyar APC ya gaza komawa majalisar a 2019 bayan rashin jituwa ya shiga tsakaninsa da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Tuna baya: A 2019, FFK ya ce gara ya sheka lahira da ya koma APC

Labari Da Duminsa: Sanata Shehu Sani Ya Koma Jam'iyyar PDP
Sanata Shehu Sani. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Rikicin da ke tsakaninsu ya saka Sani ya gaza samun tikitin takara a jam'iyyar APC, hakan ya tilasta masa komawa jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP) inda ya yi takara amma ya sha kaye.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa Sani ya fice daga PDP amma bai bayyana sabuwar jam'iyyar da zai shiga ba.

Da ya ke tabbatar da komawarsa PDP, hadiminsa, Malam Suleiman Ahmed ya ce:

"Eh, Daga karshe Sanata Shehu Sani ya koma jam'iyyar PDP amma sai nan da makonni biyu za a yi bikin tarbarsa a hukumance idan komai ya tafi yadda aka tsara."

Ya ce Sani ya tabbatar da komawarsa PDP ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumban 2021, a lokacin da ya yi taro da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a jihar Kaduna a eewar rahoton na Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

Yanzu-Yanzu: Tsohon Minista Mai Sukar Gwamnatin Buhari, Fani-Kayode ya koma Jam'iyyar APC

A wani labarin mai kama da wannan, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa.

Shugaban kwamitin riko na APC, Mai Mala Buni ne ya gabatar da Fani-Kayode ga shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis kamar yadda kakakin Buhari Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Fani-Kayode ya ce yana da abokai da jam'iyyu da dama kuma a halin yanzu yana zawarcin Ifeanyi Ugwuanyi, gwamnan jihar Enugu, Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo da Bala Mohammed na jihar Bauchi su shigo APC.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel