Jerin jiga-jigai 11 daga yankin kudu da suka daura damarar kubutar da Nnamdi Kanu
- Rahotanni sun bayyana cewa, ana sa ran wasu jiga-jigan siyasa a yankin Igbo za su tsaya wa Nnamdi Kanu kan shari'arsa
- A rahotannin da muka samo, mun tattaro muku sunayen wasu manya daga yankin kudu da suka zauna don taimakawa Kanu
- A jerin mutanen 11, kowa mai rike da mukami ne a majalisar tarayyar Najeriya, kuma ana damawa dasu a gwamnati
Abuja - Sanatocin daga yankin kudu maso gabas a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba, sun dauki matakin shiri don kafa kwamitin da zai binciki lamarin Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB domin a samu damar sakinsa
Shirin, a cewar The Sun, shine tattaunawa da hukumomin gwamnatin tarayya da suka dace kan ci gaba da tsare Kanu.
Wadanda ke cikin wannan matakin sun hadu a gidan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu a babban birnin tarayya Abuja.
Jiga-jigan na kabilar Igbo sun ce makasudin tsoma baki cikin aikin hukumomin shine don nemo mafita ta siyasa kan lamarin, in ji Premium Times.
Jiga-jigan da suke fatan tsayawa Nnamdi Kanu
Legit.ng ta tattaro jerin wadannan jiga-jiga 'yan majalisar tarayya da suka ci alwashin nemo wa Nnamdi Kanu mafita.
Ga su kamar haka:
1. Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Enyinnaya Abaribe
2. Sanata Uche Ekwenife,
3. Ifeanyi Ubah
4. Chukwuka Utazi
5. Theodore Orji, mataimakin shugaban marasa rinjaye
6. Mataimakin Shugaban marasa rinjaye na majalisa, Tobi Okechukwu
7. Mai magana da yawun majalisar wakilai, Benjamin Kalu
8. Nkeiruka Onyejeocha
9. Obinna Chidioka
10. Chinedu Ogar
11. Igariwe Iduma
Kakakin majalisa ya musanta kwatanta IPOB, 'yan Yarbawa da Boko Haram
A wani labarin, Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya yi watsi da wasu rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa da ke cewa 'yan arewan IPOB da Yarbawa duk daya ne da Boko Haram da ISWAP.
Lanre Lasisi, mai magana da yawun Gbajabiamila, ya yi karin haske a cikin wata sanarwa da aka aike wa Legit.ng a daren Laraba, 15 ga Satumba.
Ya bayyana cewa:
“Babu inda Shugaban Majalisar ya ambaci sunan wata kungiya. Abin da ya fito fili a cikin jawabin Shugaban Majalisar shi ne mayar da hankali kan ayyukan miyagun mutane da masu aikata laifuka, da tasirin su ga kasar.”
Asali: Legit.ng