PDP ta samu abin yin magana, Ministan Buhari yace ana sata salin-alin a Gwamnatin APC

PDP ta samu abin yin magana, Ministan Buhari yace ana sata salin-alin a Gwamnatin APC

  • Jam’iyyar PDP ta maida martani a kan wasu kalamai da Rotimi Amaechi ya yi
  • Ministan yace watakila a samu wadanda ke sata a boye a Gwamnatinsu ta APC
  • PDP tace wannan ya tabbatar da abin da ta ke fada kan satar da ake ta tafkawa

Abuja - Jam’iyyar adawa ta PDP tace bayanan da aka ji Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya na yi a kan gwamnatin APC, sun tabbatar da abin da ta ke fada.

Yadda Amaechi ya wanke PDP - Kola Ologbondiyan

PDP ta bakin Mai magana da yawunta, Kola Ologbondiyan ta ce abin da Ministan tarayyar ya fada, ya gaskata ikirarinta na cewa ana sata a gwamnatin nan.

A ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021, jaridar The Cable ta rahoto sakataren yada labaran na APC, Kola Ologbondiyan, ya na maida wa Ministan martani.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

Jam’iyyar hamayyar tace kalaman Ministan sun tabbatar da barna da rashin gaskiyar da ake yi a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Abin da Amaechi ya ambata ya nuna sata a boye yana cikin tarihin da APC za ta bari a mulki.”
“Wannan ya nuna abin da ya sa gwamnatin nan ta buge da furofaganda, ta gagara gurfanar da jami’anta da shugabannin APC da aka samu da rashin gaskiya.”

Buhari
Buhari a Aso Rock Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

PDP ta kalubalanci gwamnatin Buhari

Premium Times tace PDP ta kalubalanci shugaba Buhari ya yi bincike a kan jagororin APC da ake zargi da hannu a bacewar Naira tiriliyan 25 daga baitul-mali.

Jam’iyyar tace APC ta sace arzikin kasa, ta jefa ta a matsin tattalin arziki sau biyu a cikin shekaru shida, ta sa Najeriya ta zama hedikwatar talauci a Duniya.

Kara karanta wannan

Shugabannin PDP sun zauna da Goodluck Jonathan, sun roke shi ka da ya jefar da Jam’iyya

PDP ta ce an sace Naira tiriliyan 9.3 a NNPC, bayan biliyoyin kudin makamai da NSA yace sun bace, da kudin da aka sata daga NHIS da NEMA a mulkin APC.

Ologbondiyan ya tabo zargin kudin da suka yi kafa a asusun hukumomin NPA, NIMASA, FMBN da FIRS da tsarin SIP, ya yi kira ga jama’a su guje wa APC a 2023.

Me Rotimi Amaechi ya fada?

Da aka yi hira da Amaechi kwanaki, yace babu mamaki akwai wasu da ke satar dukiyar gwamnati a boye, akasin abin da ya faru a lokacin mulkin PDP.

Ba kamar gwamnatin baya ba, wannan gwamnatin idan zaka saci kuɗi sai dai ka yi a sirrince. Ministan yace gwamnatinsu ta fi kowace gwamnati rike amana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel