Yadda Buhari ya sanya ni barin PDP zuwa APC, Gwamna Dave Umahi ya magantu (Bidiyo)

Yadda Buhari ya sanya ni barin PDP zuwa APC, Gwamna Dave Umahi ya magantu (Bidiyo)

- Gwamna Dave Umahi ya alakanta sauya shekarsa da kulawar Shugaban kasa Muhammadu Buhari gareshi tamkar uba

- Gwamnan na Ebonyi ya wofantar da ikirarin cewa ya bar PDP ne saboda ya zama Shugaban kasa a 2023

- Umahi ya jinjinawa Shugaban kasar wanda ya bayyana a matsayin “ubangida, Uba kuma aboki” cewa bai yi danasanin komawa tafiyar jam’iyya mai mulki ba

Daga karshe Dave Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya bayyana dalilinsa na sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Yayinda ya bayyana a shirin Arise TV a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, Umahi ya bayyana ikirarin cewa PDP ce ta kai shi matsayin da yake kai a matsayin “shirme tsantsa.”

KU KARANTA KUMA: Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera

Gwamnan, wanda ya dade da zama dan gaban goshin APC bayan sauya shekarsa, ya bayyana cewa ya koma tafiyar APC ne saboda halin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na zame masa “uba”.

Idan za a tuna, jam’iyyar mai mulki ta tabbatar da sauya shekar Umahi a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba.

Gwamnan ya raba jaha da jam’iyyar adawa lamarin da ya sanya PDP cikin alhini kasancewarsa fitila mai haskawa a jam’iyyar.

Yadda Buhari ya sanya ni barin PDP zuwa APC, Gwamna Dave Umahi ya magantu (Bidiyo)
Yadda Buhari ya sanya ni barin PDP zuwa APC, Gwamna Dave Umahi ya magantu (Bidiyo) Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

Tuni dai Umahi, wanda ya kasance Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas ya fara shan caccaka daga mambobin tsohuwar jam’iyyarsa ciki harda Nyesom Wike wanda ya ce ya sauya sheka ne don ya zama Shugaban kasa.

Amma da yake karin haske kan sauya shekarsa, gwamnan ya yi watsi da ikirarin cewa PDP ce ta kai shi matsayin da yake kai.

Ya jadadda cewa ya bayar da gagarumin gudunmawa a jam’iyyar mai adawa ciki harda shawarar kawo Godwin Obaseki a lokacin gwagwarmayarsa a APC.

KU KARANTA KUMA: Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera

“Mutane ne ke samar da jam’iyya. Na bayar da gudunmawa wajen samar da PDP ba akasin haka ba. Na kasance mai wanzar da zaman lafiya da sasanci.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari gidan wani tsohon gwamna, sun kashe dan sanda

“PDP na so na matsawa Shugaban kasa. Amma bani da wani ubangida sama da Shugaban kasa. Shi (Buhari) ne ubangidana, ubana, abokina, kuma ban yi danasani a kan haka ba.

“Ya kasance mai adalci ga wadanda ke sukarsa a koda yaushe, shiyasa ya zamo uba, don haka, ina farin cikin yin abunda nake yi.”

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa David Umahi, gwamnan Ebonyi, saboda chanja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

A ranar Talata, Umahi ya bayyana komawa APC, yana mai cewa ya bar tsohuwar jam'iyyar sa saboda rashin adalci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel