Dalilin da Yasa Muka Kashe Ɗan Sanatan APC, Abdul Na'Allah, Matasan da Aka Cafke Sun Yi Bayani

Dalilin da Yasa Muka Kashe Ɗan Sanatan APC, Abdul Na'Allah, Matasan da Aka Cafke Sun Yi Bayani

  • Mutanen da aka cafke da hannu a kisan ɗan sanatan APC, Abdulkareem Na'Allah, sun bayyana abinda suka je yi gidan
  • Bashir Muhammad, da Nasiru Salisu, sun ce satar motar mamacin suka je yi gidan kuma sun yi rigima da shi, daga baya suka ɗaure shi
  • Kakakin yan sandan Kaduna, Muhammad Jalige, yace ana cigaba da bincike, kuma za'a gurfanar da su gaban kotu

Abuja - Matasa biyu da aka cafke da zargin hannu a kisan ɗan Sanata Na'Allah, Bashir Muhammad mai shekara 23, da Nasiru Salisu mai shekara 27, sun bayyana dalilin da yasa suka kashe shi.

Da yake zantawa da manema labarai a hedkwatar yan sanda dake Abuja, wanda ake zargi, Bashir Muhammad, yace sun shiga gidan marigayin ne da niyyar sace motarsa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Janar Faruk Yahaya: Za mu ji da 'yan bindiga da yaren da suke fahimta

Dan sanata Na'Allah
Dalilin da Yasa Muka Kashe Ɗan Sanatan APC, Abdul Na'Allah, Matasan da Aka Cafke Sun Yi Bayani Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bashir, wanda ya yi ikirarin cewa bai san wanda suka kashe ba, yace:

"Mun zo wucewa ta gidan mu uku, ni da Nasiru da Usman Dan-Kano, sai idon mu yakai kan wata mota da aka ajiye a cikin gidan."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dan-Kano yace zamu dawo ɗauke motar nan. Washe gari ana maka ruwan sama, muka samu damar shiga gidan, muka hau kan rufin gidan, sannan muka cire kusoshi, muka yiwa kanmu hanya."
"Bayan mun shiga gidan, ni da Nasiru muka buɗewa Usman kofa, wanda ke rike da fitili, hasken wannan fitilar ya jawo hankalin shi, ya ɗakko wani abu daga gadonsa, suka fara kokawa da Nasiru."
"Yayin wannan taƙaddamar ne sai mutumin ya faɗi, nan take muka yi amfani da abin sagale kaya muka ɗaure shi, domin kada ya tona mana asiri. Daga nan muka ɗauki makullan motar muka fece."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afka gidan gona, sun sace wani babban ɗan kasuwa, sun bindige wani mutum

Yadda na shiga cikin lamarin - Salisu

Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Nasiru Salisu, ya bayyana cewa abokinsa Bashir ne ya saka shi cikin Operation ɗin.

Salisu, wanda ke zaune a Anguwar Kawo Kaduna, yace Bashir ne ya ɗaure ɗan sanatan bayan faɗan da suka yi.

Salisu yace:

"Na siyo buhunan shinkara 23 da kuɗin dana samu bayan satar, amma jami'an kwastam suka kwace."

Mutum nawa yan sanda suka kama?

Da yake shigar da waɗanda ake zargi mutum 25 a jihar Kaduna, kakakin yan sandan jihar, ASP Muhammad Jalige, yace mutanen da aka kama da zargin kisan gillan sun amsa laifinsu.

Ya ƙara da cewa sun siyar da motar a Jamhuriyar Nijar kan kudi miliyan ɗaya, inda suka raba kuɗin a tsakaninsu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Jalige yace har yanzun ana cigaba da bincike domin kamo ragowar waɗanda ake zargi, kuma za'a gurfanar da su gaban kotu.

Kara karanta wannan

Yadda Yan bindiga suka yi awon gaba da Sarkin Bungudu a titin Kaduna/Abuja

A wani labarin kuma Wani ɗan majalisar wakilai daga jihar Ribas ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, shine ya karanta wasikar sauya shekar ɗan majalisar a zaman yau Alhamis.

Shugaban masu rinjaye, Ado Doguwa, yace akwai sauran mambobin PDP da zasu koma APC a mako mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel