'Yan bindiga sun afka gidan gona, sun sace wani babban ɗan kasuwa, sun bindige wani mutum
- 'Yan bindiga sun kai hari sun sace wani dan kasuwa mai gidan gona a Emoren-Imota
- Maharan sun tare dan kasuwan ne a lokacin da ya ke daf da shiga gidan gonarsa a mota
- Maharan sun kuma harbi wani mutum a unguwar yayin da suka tafi sace dan kasuwar
'Yan bindiga sun sace wani mai gidan gona, Jide Lawal, a gidan gonarsa da ke unguwar Agohun, Emoren - Imota, wani gari da ke kan iyakar jihar Legas da Ogun, The Punch ta ruwaito.
Punch Metro ta ruwaito cewa Lawal ya ziyarci gidan gonarsa ne a ranar Laraba don duba yadda abubuwa ke tafiya, amma sai wasu mutane da bindiga suka tare shi a kofar shiga.
An ce dan kasuwan na jira mai gadi ya bude masa kofa ne a lokacin da maharan suka yi amfani da damar suka tare shi.
Nan take suka nuna masa bakin bindiga suka bukaci ya yi saranda.
A lokacin da mai gadi ya bude kofa, maharan su uku da bindigu suka shigar da Lawal cikin gidan gonar.
Wani mai kula da gidan gonar, Ahmed Saliu, ya ce 'yan bindigan sun tsere da Lawal ne ta cikin daji da ke kusa da gonar.
Ya ce:
"Muna cikin gidan gonar a lokacin da Mr Lawal ya iso kofa ya latsa hon domin a bude masa. Mai gadi na budewa sai ya gan shi tare da mahara uku dauke da bindiga suka shigo da Mr Lawal.
"Sun umurci mu kwanta a kasa sannan suka tafi da mai gidan mu. Mun kai rahoto ofishin 'yan sanda na Imota kuma mun sanar da iyalan mai gidan namu."
Wani manomi a yankin mai suna Biodun ya ce sace Lawal ya tada hankalin mutane, ya kara da cewa maharan sun harbi wani mutum da ke wucewa yayin da suka taho sace mai gidan gonar.
Abin da 'yan sanda suka ce game da lamarin?
Kwamishinan 'yan sanda Legas, Hakeem Odumosu, ya ce lamarin ya faru ne a jihar Ogun, ya kara da cewa gidan gonan yana garin Agbohun ne.
Amma kuma kakakin yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce an tafka laifin ne a Imota, jihar Legas.
Ya ce:
"DPO da ke kula da yankin ya ce lamarin ya faru ne a Imota, Legas hakan yasa ba a shigar da rahoto a ofishinsu ba.
'Yan Bindiga Sun Sace Sakataren NASIEC a Nasarawa
A wani labarin daban, Ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Mohammed Okpu, sakataren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Jihar Nasarawa, The Cable ta ruwaito.
Hakan na cikin wata sanarwar ne da mai magana da yawun yan sandan jihar Nasarawa, Rahman Nansel, ya fitar a ranar Laraba a Lafia.
The Cable ta ruwaito cewa Nansel ya ce kimanin yan bindiga biyar ne suka kutsa gidan sakataren na NASIEC a ƙauyen Bakin Rijiya da ke hanyar Lafia-Shendam misalin ƙarfe 11.45 na daren Talata.
Asali: Legit.ng