Da Dumi-Dumi: Shugaban Majalisar Dattijai Ya Rantsar da Sabon Sanatan Jam'iyyar PDP
- Shugaban majalisar dattijan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya bada rantsuwar kama aiki ga sabon sanata daga Cross Rivers
- Sanatan wanda kotun koli ta tabbatar da sahihancin takararsa karkashin PDP, ya fara aiki ne ranar Laraba
- Sanata Agom Jarigbe zai maye gurbin wanda aka rantsar da farko, Steven Odey, daga mazaɓar Cross Rivers ta arewa
Abuja - Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ranar Laraba, ya rantsar da sabon sanatan jam'iyyar PDP, Agom Jarigbe, wanda zai maye gurbin, Stephen Odey, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Jarigbe na jam'iyyar hamayya ta PDP, ya jima suna fafatawa a shari'a da Steven Odey, kan waye halastaccen ɗan takarar da jam'iyya ta tsayar a zaɓen cike gurbin sanatan Cross Rivers ta arewa.
Jarigbe ya amshi rantsuwar fara aiki daga shugaban majalisar bayan samun nasara a kotun ƙoli ta ƙasa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Meyasa INEC ta gudanar da zaɓen cike gurbi?
Legit.ng Hausa ta gano cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, ta gudanar da zaɓen maye gurbi ne a mazaɓar Cross Rivers ta arewa bayan mutuwar sanata Rose Oko.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai kotun ɗaukaka ƙara dake zamanta a Kalaba, babban birnin jihar, ta bayyana, Jarigbe Agom Jarigbe a matsayin ɗan takarar da ya lashe zaben cike gurbi na ranar 5 ga watan Disamba, 2020.
Kotun bisa jagorancin mai shari'a Chioma I. Nwosu, ta bada umarnin a ba shi satifiket ɗin zaɓe, wanda da farko hukumar INEC ta baiwa, Steven Odey.
Bugu da kari kotu ta umarci INEC ta kwace satifiket ɗin daga hannun wanda ta baiwa da farko, ta baiwa wanda hukuncin kotu ya tabbatar a matsayin zaɓaɓɓen sanata.
A wani labarin na daban kuma Ministan Buhari ya fallasa yadda ake amfani da jiragen alfarma wajen satar albarkatun Zinari a Najeriya
Ministan hakar albarkatun ƙasa, Dakta Uche Ogah, ya bayyana irin ta'adin da ake yi ta hanyar amfani da jirage masu zaman kansu.
Ogah yace dole sai an samar da hukunci mai tsauri kan duk waɗanda aka damke da hannu a safarar zinari ba bisa ka'ida ba.
Asali: Legit.ng