Dalilin da Yasa Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Aso Rock, Pantami

Dalilin da Yasa Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Aso Rock, Pantami

  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya bayyana dalilin da yasa shugaban EFCC ya yanke jiki ya faɗi
  • Abdulrasheed Bawa ya yanke jiki ya faɗi ne yayin da yake jawabi a fadar shugaban ƙasa, an gaggauwa bashi agajin gaggawa
  • Pantami ya alaƙanta faɗuwar bawa da takurawa kansa da yayi da kuma ayyukan da suka masa yawa

Abuja - Babban dalilin da yasa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya yanke jiki ya faɗi yayin da yake jawabi a fadar shugaban ƙasa ya fito fili.

Vanguard ta ruwaito cewa Bawa, wanda ya matsa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ya yanke jiki ya faɗi yau Alhamis.

Rahoto ya nuna cewa an yi gaggawar kai shugaban EFCC zuwa asibitin dake cikin Aso Rock domin samun agajin lafiya cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Abdulrasheed Bawa yana cikin koshin lafiya - EFCC

Shugaban EFCC, Bawa, Tare da Pantami
Dalilin da Yasa Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Aso Rock, Pantami Hoto: decencyglobalnews.blog
Asali: UGC

Da yake martani kan lamarin, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Pantami, ya alaƙanta faɗuwar da takurawa kai da kuma yawan aiki.

Ministan ya yi kira ga yan Najeriya su saka Bawa cikin addu'o'insu, ya bayyana cewa shugaban ya samu kulawar da ta dace kuma ya dawo hayyacinsa.

Wane hali Bawa yake ciki?

Bayan wasu yan mintuna da kai Bawa asibitin cikin Aso Rock, Kakakin hukumar EFCC, Mr. Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa shugabansu yana cikin koshin lafiya.

Kakakin EFCC yace:

"Shugaban EFCC, Albdulrasheed Bawa, yana cikin koshin lafiya. Bayyana haka ya zama wajibi biyo bayan abinda ya faru a yau 16 ga watan Satumba, a fadar shugaban ƙasa, lokacin da yake jawabi."
"Bayan abinda ya faru, Bawa ya samu kulawar lafiya cikin gaggawa kuma tuni ya koma kan kafafunsa."

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

A wani labarin kuma Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu kasashe 6 da Allah ke nuna ikonsa, inda ake shafe tsawon lokaci ana rana, babu dare

Ƙasahen turawa, Finland da Sweden na daga cikin jerin ƙasashen duniya shida, waɗanda rana bata faɗuwa na tsawon wani lokaci.

Punch ta ruwaito cewa waɗan nan kasashen na fuskantar zafin rana na tsawon watanni ba tare da ta faɗi ba kuma wasu na fuskantar duhun dare na yan kwanaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262