'Kungiyar Kiristocin Nigeria, CAN, ta jinjinawa Pantami: Muna alfahari da kai a matsayin ɗan mu

'Kungiyar Kiristocin Nigeria, CAN, ta jinjinawa Pantami: Muna alfahari da kai a matsayin ɗan mu

  • A wata wasika wacce sakataren kungiyar kiristoci ta Najeriya, Senior Apostle John Adedigba ya sa hannu ya yaba wa Pantami
  • A cikin wasikar, kungiyar CAN ta kira ministan sadarwa, Isa Ali Pantami da dan ta yayin taya shi murnar karin girman da ya samu
  • Ministan ya samu karin girma inda ya zama farfesa a harkar tsaron yanar gizo kamar yadda rahotanni suka tabbatar

Jihar Gombe - Kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Gombe ta kira ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami da dan ta, SaharaReporters ta ruwaito.

A cikin wata wasika wacce sakataren kungiyar, Senior Apostle John Adedigba ya sanya hannu a madadin duk sauran ‘yan kungiyar ya kira Pantami da dan su.

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, kungiyar kiristocin Najeriya ta reshen jihar Gombe ta taya ministan sadarwa, Isa Ali Pantami farin cikin samun karin girma zuwa farfesa a harkar tsaron yanar gizo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

'Kungiyar Kiristocin Nigeria, CAN, ta jinjinawa Pantami: Muna alfahari da kai tamkar ɗan mu
Ministan Sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Pantami. Hoto: SaharaReporters
Asali: Twitter

Kungiyar CAN ta jihar Gombe ta bayyana alfaharin da take yi da Pantami

CAN ta jihar Gombe ta kara da bayyana yadda Pantami ya samu tarin nasarori daga hawan sa kan mulki zuwa yanzu inda ta bayyana alfaharin da take yi da shi.

Kamar yadda takardar tazo, kuma Sahara Reporters suka ruwaito:

“A maimakon daukacin kungiyar kiristoci da ke jihar Gombe, muna farin cikin taya dan mu kuma dan’uwan mu Farfesa Isa Ali Pantami FNCS, FBCS, FIIM, MCPN, kuma mai girma ministan sadarwa bisa samun karin girman da kayi na zama farfesa a fannin tsaron yanar gizo da kuma cika shekaru 2 a kan kujerar ka.
“Muna taya ka, iyalin ka, jihar Gombe da Najeriya gabadaya murnar samun wannan ci gaba, muna alfahari da ka kasance dan jihar Gombe kuma muna addu’a hakan ya kasance mai amfani ga Najeriya da mutane gaba daya.

Kara karanta wannan

Coci ya ruguje kan masu bauta ana cikin ibada a Taraba, ya hallaka mutane biyu

“Muna sane da ci gaban da kake samar wa a matsayin ka na ministan sadarwa, kammala dubannin ayyuka sannan yanzu haka ana kan wasu ayyukan guda 400 a Najeriya kuma kai ne kake sanya ido akan su cikin shekaru 2 da kuma ci gaba da mara wa shugaba Buhari, hakika ka saka mu farin ciki, muna maka addu’a a coci da fatan Ubangiji zai ci gaba da baka nasarori cikin shekaru masu zuwa da yardar Jesus. Muna kara taya ka farin ciki.”

Duk da tarin zargin da ake yi wa ministan na kasancewa mai alaka da wasu ayyukan ta’addanci.

“Jihadi dole ne ga ko wanne mai imani, musamman a Najeriya,” kamar yadda Pantami ya dade yana fadi a wa’azin sa kafin ya zama minista.
“Ya Ubangiji, ka bai wa Taliban da Al-Qaeda nasarori,” kamar yadda ya dade yana furtawa.

Sai dai Pantami ya dade yana cewa ya janye maganganunsa kuma rayuwar sa ta canja tsawon lokaci. Ya ce ya kai shekaru 15 yana janye maganganun sa na ta’addanci.

Kara karanta wannan

Kungiyar Oyo ta gargadi sarakunan gargajiya, tana so a binciki ziyarar da Gumi ya kai jihar

Duk da janye kalaman sa, ‘yan Najeriya da dama suna ganin ya dace a tilasta Pantami ya sauka daga kujerarsa kuma ayi bincike mai tsanani akan sa.

Sai dai fadar shugaban kasa tana matukar goyon bayan sa kuma ta nuna karara cewa babu wata alamar za ta iya korar ministan tunda ya bayar da hakuri dangane da irin fahimtar sa ta baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel