Ba Zan Bada Hakuri Ba Kan Kalaman da Na Yiwa Shugaba Buhari, Gwamna
- Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, yace sam babu bukatar ya bada hakuri kan kalaman da ya yiwa shugaba Buhari
- Gwamnan ya kuma bayyana jin daɗinsa bisa ziyarar Ali Modu Sherif, wanda ke neman tikitin zama shugaban APC na ƙasa
- Umahi yace Shugaba Buhari, shi ne jagora kuma yana da damar zaɓar wanda zai shugabanci APC na gaba
Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, yace ba dalilin da zai bada hakuri kan kiran shugaba Buhari da 'Mutum mai kyakkyawar zuciya, kuma uba,' kamar yadda Punch ta ruwaito.
Umahi ya yi wannan magana ne yayin da ya karbi baƙuncin tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Ali Modu Sheriff, a gidan gwamnati dake Abakiliki.
Gwamnan ya jaddada cewa ba shi da wani dana sani kan kalamansa, kuma babu wata sukar mutane da zata canza masa ra'ayi.
Umahi yace:
"Idan mutum ɗaya yana da kyakkyawar zuciya, saura kuma basu da ita, kuma basu baiwa abu fifiko, to babu wani cigaba da za'a samu."
"Idan kuka diba mutanen da muke aiki tare a gwamnatina, zuciyarmu ta zo ɗaya, shiyasa muka samu nasara da dama."
Gwamna Umahi ya yi kira ga yan Najeriya su cigaba da goyon bayan shugaba Buhari, domin mutum ne ɗaya tilo da ya fita daban da saura wajen nagarta."
Meyasa Sherif ya ziyarci Ebonyi?
Legit.ng Hausa ta gano cewa Sheriff ya ziyarci jihar Ebonyi ne, domin neman goyon bayan gwamnan jihar kan kudirinsa na neman shugabancin jam'iyyar APC.
Gwamnan ya bayyana cewa shugaba Buhari ne kaɗai yake da ikon yanke hukunci kan waye zai zama shugaban APC na gaba.
Hukuncin da Ya Dace Yan Najeriya Su Ɗauka Kan Shugabannin da Suka Gaza Cika Alƙawari, Tsohon Ministan Sadarwa
"Ka kyauta (Sheriff) daka bayyana mana kudirinka na neman kujerar shugaban APC na ƙasa, amma shugaban ƙasa, wanda shine jagoran jam'iyya, shike da wuka da nama."
"Shi kaɗai yake da damar yanke hukunci kan shugaban APC na gaba, amma idan ya bar damar ga kowa, kai ne zaɓi na."
"Shugaban ƙasa yana da damar cewa wannan ya dace ya zama shugaban APC saboda kawo cigaba, babu gardama zamu masa biyayya."
Meyasa Sheriff ya nemi goyon bayan Umahi?
A jawabinsa, Ali Modu Sheriff, yace ya yanke sanar da gwamna Umahi kudirinsa na neman shugabancin APC ne saboda shine jagoran siyasa a kudu ta gabas.
Ya kuma yi kira ga yan Najeriya su daina maganar cewa sai ɗan wani yanki zai shugabanci Najeriya, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa ɗan takarar da ya dace kuma wanda ake tsammanin zai yi aikin da ake bukata shi ya kamata a zaƙulo kuma a mara masa baya.
A wani labarin kuma Babu Wani Ministan da Ya Ɗauki Matakan Kakkaɓe Yan Ta'adda A Najeriya Kamar Sheikh Pantami, Kayode
Fani Kayode, ya yabawa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, bisa matakan da yake ɗauka a arewa.
Tsohon ministan jiragen sama ya kuma yabawa shugaba Buhari da kuma gwamnonin arewa maso yamma bisa kokarin da suke na magance yan ta'adda.
Asali: Legit.ng