Babu Wani Ministan da Ya Ɗauki Matakan Kakkaɓe Yan Ta'adda A Najeriya Kamar Sheikh Pantami, Kayode

Babu Wani Ministan da Ya Ɗauki Matakan Kakkaɓe Yan Ta'adda A Najeriya Kamar Sheikh Pantami, Kayode

  • Fani Kayode, ya yabawa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, bisa matakan da yake ɗauka a arewa
  • Tsohon ministan jiragen sama ya kuma yabawa shugaba Buhari da kuma gwamnonin arewa maso yamma bisa kokarin da suke na magance yan ta'adda
  • Kayode, sanannen mai sukar Pantami ne a baya, amma komai ya canza tun bayan haɗuwarsu a Kano

Abuja - Tsohon ministan jiragen sama, Femi Fani Kayode (FFK), ya yabawa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami, bisa "Saka yan ta'adda cikin halin tasku," kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A wani rubutu da ya yi, Kayode, ɗan adawan da ya koma abokim ministan sadarwa, ya kuma yaba wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Tsohon ministan ya yabawa manyan mutanen biyu ne ya yin da yake tofa albarkacin bakinsa kan matakin da aka ɗauka a arewa maso yamma don kawo karshen yan bindiga.

Kara karanta wannan

Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta

Pantami, Matawalle da Kayode
Babu Wani Ministan da Ya Ɗauki Matakan Kakkaɓe Yan Ta'adda A Najeriya Kamar Sheikh Pantami, Kayode Hoto: Femi Fani-Kayode FB fage
Asali: Facebook

Shin matakan da ake ɗauka suna haifar da ɗa mai ido?

Tsohon ministan yace:

"A yan makonnin da suka shuɗe, an samu gagarumar nasara kan miyagun yan bindiga da yan ta'adda a yankin arewa maso yammacin Najeriya."
"Jihar Zamfara ne lamarin ya fi ƙamari da kuma sauran jihohin yammacin arewa da suka haɗa da Katsina, Kaduna, Sokoto, Jigawa, Kebbi da kuma jihar Neja."
"Abinda gwamnonin waɗan nan jihohin suka yi yana da ban sha'awa kuma ya sanya miliyoyin mutane cikin farin ciki a faɗin arewa da kuma ƙasa baki ɗaya."
"Ina fatan gwamnonin kudu zasu jingine siyasa, su yi koyi da matakan da gwamnonin arewa suka ɗauka don kare rayuwar mutane."

Wane matakai gwamnonin arewa suka ɗauka?

Kayode ya bayyana cewa ɗaya daga cikin matakan da aka ɗauka a Zamfara kuma ake shirin ɗauka a wasu jihohin arewa-yamma shine datse hanyoyin sadarwa.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Ya Dace Yan Najeriya Su Ɗauka Kan Shugabannin da Suka Gaza Cika Alƙawari, Tsohon Ministan Sadarwa

Kayode yace:

"Wannan matakin ya daƙile yan ta'adda da kuma aikinsu na garkuwa da mutane kuma matakin ya baiwa kowa mamaki."
"Maganar gaskiya minista Pantami ya yi namijin kokari wajen ɗaukar wannan tsattsauran mataki da haɗin kan gwamnan Zamfara."
"Babu wani minista da ya dakushe yan ta'adda da ayyukansu cikin shekara 6 kamar Pantami kuma babu wanda ya kwatanta haka cikin gaggawa kamar shi."

Alakar Pantami da Kayode ta canza Salo

Sabuwar kyakkyawar alakar Kayode da Pantami ta bayyana ga kowa ne bayan ɗaura auren ɗan shugaba Buhari a Kano watan da ya gabata.

Tsohon ministan ya tura hotonsa tare da Sheikh Pantami a kafar sada zumunta kuma ya kira shi 'Ɗan uwa.'

A wani labarin kuma ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi, ya bayyana matakin da ake ciki kan badaƙalar Ibrahim Magu

Ministan ya bayyana cewa tsohon mukaddashin shugaban EFCC ɗin yana nan a tsarin ma'aikatan gwamnatin tarayya dake ɗibar albashi.

Kara karanta wannan

Bincike: Akwai bindigogi AK-47 sama da 60,000 a sansanonin 'yan bindiga 120

Yace a halin yanzun an mika rahoton binciken kwamiti ga shugaban ƙasa, ana jiran ɗaukar mataki na karshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel