Da Jiragen Alfarma Masu Zaman Kansu Ake Amfani Wajen Satar Albarkatun Zinare a Najeriya, Minista Ya Fallasa

Da Jiragen Alfarma Masu Zaman Kansu Ake Amfani Wajen Satar Albarkatun Zinare a Najeriya, Minista Ya Fallasa

  • Ministan hakar albarkatun ƙasa, Dakta Uche Ogah, ya bayyana irin ta'adin da ake yi ta hanyar amfani da jirage masu zaman kansu.
  • Ogah yace dole sai an samar da hukunci mai tsauri kan duk waɗanda aka damke da hannu a safarar zinari ba bisa ka'ida ba
  • Hakazalika ya bayyana wasu matakai da matukar aka bi su za'a kawo karshen hakar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba da safararsu

Abuja - Karamin ministan hakar ma'adanai, Dakta Uche Ogah, ya bayyana cewa ana amfani da jirage masu zaman kansu wajen safarar zinare ba bisa ƙa'ida ba a Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ministan ya faɗi haka ne a wani zama don ji kan dala biliyan $9bn da aka rasa ta hanyar fasa kwaurin zinari da kuma hako ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Kwamitin albarkatun ƙasa da hakar ma'adanai na majalisar dattijan Najeriya, shine ya shirya taron a Abuja.

Jirgin sama
Da Jiragen Alfarma Masu Zaman Kansu Ake Amfani Wajen Satar Albarkatun Zinare a Najeriya, Minista Ya Fallasa Hoto: theguardian.com
Asali: UGC

Ministan ya bukaci a hukunta duk wani mai hannu kan aikata irin wannan laifin, Dakta Ogah yace:

"Ana amfani da jirage masu zaman kansu wajen satar zinari, wannan dalilin yasa wajibi a sanya ido kan masu jiragen sama da ayyukan jiragen."

Me satar zinare zai jawo wa Najeriya?

Ministan ya kara da cewa smogan zinari da hakar ma'adanai ba bisa doka ba yana ƙara janyo wa Najeriya asarar biliyoyin daloli duk shekara.

A cewar ministan, lamarin na ƙara yawa ne saboda haɗin kan hukumomin tsaro da masu aikata laifin, haɗin kan al'ummar yankunan dake da albarkatun, karancin fasahar zamani da kuma rashin kishin ƙasa da yan Najeriya ke nunawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar

Ta wace hanya za'a magance matsalar?

This day ta rahoto, Ministan yace:

"Idan anason kawo karshen wannan laifin, wajibi a ɗauki matakan hukunci mai tsauri kan duk wanda aka kama da hannu."

Ya kuma kara da cewa za'a iya magance matsalar ta hanyar samar da yan sandan hakar ma'adanai, kotu na musamman ko kuma masu hukunta laifuka, ƙara kasafin ma'aikata da kuma kishin ƙasa daga wurin yan Najeriya.

A wani labarin kuma Dan Majalisar Tarayya Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Majalisa Ta Tafi Hutu Saboda Jimami

Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta sanar da ɗage zamanta zuwa 15 ga watan Satumba, 2021, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Majalisar ta dauki wannan matakin ne biyo bayan mutuwar ɗaya daga cikin mambobinta, Adedayo Omolafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262